Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara cewa jam’iyyar APC ba ta yi zaben fidda gwani a jihar ba.
Jam’iyyar APC ta garzaya kotun Koli domin kalubalantar wannan shari’a.
A zaman kotun Koli, yau Juma’a ta amince da wannan hukunci da kotun daukaka kara ta yanke. Ta tabbatar da hukuncin.
Yanzu dai gaba daya babu dan takara ko da daya ne tak daga jam’iyyar APC a jihar Zamfara. Hakan ya nuna cewa duk wanda yazo na biyu a zaben da aka yi shine zai dare kujerar gwamnan da sauran mukamai.
Discussion about this post