Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada tsohon Ministan Cinikayya, Bello Maitama-Yusuf a matsayin daya daga cikin mambobin Hukumar Daraktocin Jiragen Kasa na Najeriya (NRC).
Bello mai shekaru 72, an taba zargin sa da cin rashawa a zamanin mulkin soja na Shugaba Muhammadu Buhari, a cikin 1984.
Wannan ya sa Bello ya fice daga Najeriya, ya nemi mafaka a kasar waje.
Cikin 1979 Bello ya rike mukamin Ministan Harkokin Cikin Gida, sannan cikin 1982 aka maida shi Ministan Cinikayya.
Bello da marigayi Umaru Dikko sun kasance a sahun farko na jerin sunayen wadanda suka gudu daga Najeriya, kuma gwamnatin mulkin soja a lokacin ta neme su ruwa a jallo.
Bayan sama da shekaru 30, a yanzu an nada shi mamba na Hukumar Daraktocin Kula da Jiragen Kasa.
Ibrahim Hassan ne shugaban hukumar, sauran mambobi sun hada da Kayode Opeifa, AIG Umar Ambursa, Obiarari Nnamdi da sauran su.
Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ne ya bada sunan sa, shi kuma Buhari ya amince.
Haka Kakakin Yada Labarai na Badaru a fannin Soshiyal Midiya, Auwal Sankara ya rubuta a shafin san a Facebook.
Ya ce an nada Bello Maitama saboda “kwazon sa da juriya da kuma aiki tukuru wajen tsayawa tsayin-daka domin ci gaban jam’iyyar APC da kuma ciyar da Najeriya da Jihar Jigawa gaba.”
Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya kaddamar da hukumar daraktocin tun a ranar Alhamis da ta wuce.
Discussion about this post