Zababben Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa a shirye yake ya binciki duk wani da ake zargin ya yi rashin gaskiya a karkashin mulkin Gwamna Jibrilla Bindow mai barin gado.
Fintiri ya bayyana haka a Yola, ranar Asabar a lokacin da ya ke karbar rahoto mai dauke da shafuka 67, wanda Kwamitin Karbar Mulki ya damka masa.
Ya kara da cewa binciken da kwamitin ya gudanar ya nuna akwai wurare da dama inda aka yi almubazzaranci da kudaden gwamnati.
Don haka ya ce ba zai yiwu ba sabuwar gwamnatin da zai kafa ta kauda kai daga wannan tabargaza da aka tafka ba.
“Za mu mike tsaye mu fuskanci wannan babban kalubale dake a gaban mu, tare da cikakkar masaniyar cewa dama an zabe mu ne domin mu zo mu gyara barnar da aka yi. Ba za mu kauda kai daga wuraren da aka karya doka ba, ko wuraren da aka yi facaka da kudade ko kuma inda wadanda aka baiwa amana suka tafka zamba.
“Jihar Adamawa, wadda ita ce abin alfaharin mu, kuma gidan mu na gado, an wayi gari an lalata ta, an ji mata ciwon da aka daddauje mata fuska. Amma dai mu na da yakinin cewa za mu sa mata bandeji da magani, kuma za mu yi jiyyar ta har ta murmure.
“Ina kara nanatawa domin kowa ma ya saurara da kyau. Ina kiran jama’ar mu mu tashi mu hada kai domin mu dora karayar da aka yi wa Jihar Adamawa. Wurin wannan aikin dorin kuwa, ba zan damu na taka kafar duk wani da muka samu ya gitta kafar sa a hanyar da za mu bi mu yi aikin mu ba.” inji Fintiri.
Ya nuna takaicin yadda gwamnati mai barin gado ta karbi kusan naira biliyan 332 a cikin shekaru hudu daga gwamnatin tarayya, amma babu wani abin kirkin da za a iya gani a nuna a cikin jihar da za a iya tutiya da shi.
Da ya ke mika rahoton, Shugaban Kwamitin, Aliyu Ismaila, ya bayyana cewa gwamnatin Bindow ta yi raga-raga da jihar, kuma ta bar dimbin bashi har na naira bilyan 115.