Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa EFCC na Farko, Nuhu Ribadu, ya ce ana yawan yi wa gwamnoni binciken kwakwaf dangane da zargin harkalla ne, saboda suna rike da asusun da ke cike da makudan kudade masu yawan gaske.
“Ku ne ke da hakkin tafiyar da gwamnatin ku. Ku ne kuma ke rike da komai na dukiya, albarkatu da makudan kudaden jiha, har ma da na kananan hukumomi.” Cewar Ribadu.
Ya yi wannan tsinkaye ne a lokacin da ya ke jawabi wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya wa zababbun gwamnoni, jiya Talata, a Abuja.
Daga nan sai Ribadu ya nanata cewa babu yadda za a yi a ce gwamnoni ba a bincike su ba.
Ya ce kai hatta ma wanda suka zabo da kan su domin ya gaje su, zai iya binciken su, kamar yadda tarihi ya nuna ba da dadewa ba a baya.
Daga nan sai Ribadu ya ce jami’an tsaro na duniya su na bibiyar duk lunguna da sako-sakon da kudade ke shiga, saboda yawaitar safarar muggan kwayoyi, ta’addanci da ya buwayi duniya da kuma shugabanni masu wawurar kudade.
Ya ce dalili kenan ake sa ido sosai a kan komai yanzu a duniya, musamman a kan shugabannin siyasa a duk inda suka shiga.
“Idan ku ka fita zuwa kasashen waje, kallon ku kawai su ke yi tsaf a tsanake. Duk abin da ku ke yi, su na sane da ku, kuma sun a bibiyar ku.
A nan Najeriya kuma Ribadu cewa ya yi hukumomin hana cin hanci da rashawa na kai farmaki da kuma bincike ne saboda majalisar tarayya ta kasa wajen bin diddigin yadda gwamnonin jihohi ke karkashe kudaden da ake bai wa kowace jiha.
Babbar hanya mafita inji Ribadu, ita ce kawai gwamna ya tabbatar da ya rike aikin sa da amana, kuma ya kare mutuncin sa daga taba dukiyar al’umma tare da yin adalci da riko da gaskiya.
Discussion about this post