A shafe tarihin wadanda suka soke koyar da tarihi a makarantun Najeriya – Wole Soyinka

0

Mashahurin marubucin nan da ya taba cin babbar lambar yabo ta duniya, Wole Soyinka, ya yi kira da a shafe tarihin dukkan wadanda suka bada shawarar a daina koyar da darasin tarihi a makarantun Najeriya.

Soyinka ya nuna bacin rai dangane da abin da ya kira rashin sanin alkibla da rashin kaifin tunani da har ya kai a ke wa darussan tarihi rikon sakainar kashi.

Ya nuna wannan bacin rai a lokacin da ya ke jawabi a wurin wani taro da bankin UBA ya shirya a Lagos domin tunawa da zagayowar Ranar Afrika.

“Shi fa tarihi ya na da nauyi sosai, shi ya sa wasu ke gudun sa.

“Na firgita sosai a cikin shekarun baya da wani sullutun minista ya bada shawarar wai a soke darasinn tarahi, a daina koyar da shi a makarantun mu. To irin wadannan mutanen su ne ma ya kamata a shafe tarihin su a doron kasa gaba daya.”

An dai daina koyar da tarihi a makarantun kasar nan shekaru da dama, sai cikin shekarar karatu ta 2018/2019 ne aka dawo da koyar da shi a cikin makarantun kasar nan.

Daga nan sai Soyinka ya nuna muhimmancin hadin kai ga kasashenn Afrika, inda ya nuna Afrika tamkar tsintsiya ce, wadda sai tana dunkule a wuri daya za ta iya share matsalolin da ke damun nahiyar Afrika.

Ya ce duk da bambancin yaruka daban-daban a fadin Afrika, wannan bai zama wata matsala wajen hadin kan al’umma da kuma kasashen na Afrika ba.

Daga nan sai ya ce hadin kai shi ne wajibi, ba ruruta abin da zai wargaza hadin kai a nahiyar Afrika ba.

A wurin wanda Shugaban Bankin UBA, Tony Elumelu da Femi kudi da kuma wasu manyan masana daga kasashen Afrika suka halarta, Soyinka ya nuna fargaba dangane da tabarbarewar tsaro a halin yanzu a fadinn kasar nan.

Ya ce Najeriya ya mirgina cikin wani kwazazzabon da tsamo ta sai an yi da gasken-gaske. Kuma inji shi, ba a taba samun tabarbawar matsalar ba kamar a wannan hali yanzu da ake ciki

Share.

game da Author