A dalilin barkewar rikici a tsakanin mazauna wasu unguwanni a jihar Bauchi, gwamnatin jihar ta saka dokar hana zairga-zirga a wadannan unguwanni.
Sakataren gwamnatin jihar Nadada Umar ne ya sanar da haka yana mai cewa daga ranar Juma’a mutanen unguwannin Gudum Fulani, Gudum Hausawa, Gudum Sayawa da Bigi za su rika zirga-zirga ne daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na Yamma.
Nadada ya ce mazauna unguwannin sun tada fitina a tsakanin su ne daga musu.
Abin dai ya kazanta da har sai da jami’an tsaro suka kawo wa mazauna unguwannin dauki.
Gwamnati ta ce saboda kada abin ya wuce gona da iri ne ya sa aka saka dokar hana zairga-zirga a wadannan unguwannin.
Gwamnati ta yi kira ga mazauna unguwannin da su tabbata basu karya wannan doka ba.