Kamar yadda aka sani cewa zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci, sannu a hankali cutar tana ta afkawa mutanen kasar nan.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa za a iya kamuwa da cutar idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar sannan idan ba a gaggauta neman magani ba cutar na iya yin ajalin mutum.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu hukumar ke kokarin ganin ta dakile yaduwar wannan cuta amma har yanzu mutane na kara kamuwa da cutar.
Daga watan Janairu zuwa 24 ga watan Maris mutane 510 sun kamu da wannan cuta inda daga ciki mutane 171 suka mutu a jihohi 21 dake kasar nan.
A yanzu haka hukumar ta ce mutane 15 sun kamu da cutar inda daga ciki mutane uku suka rasu a jihohi biyar a kasar nan.
Wadannan jihohi kuwa sun hada da Edo,Ondo,Filato,Bauchi da Taraba.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar ta hada karfi da karfe da NFELTP, ma’aikatar aiyukkan gona da ma’aikatar muhalli domin dakile yaduwar zazzabin lassa sannan hukumar za ta fi maida hankali wajen ganin cutar bai yadu zuwa jihohin Taraba da Bauchi.
Ga hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin lasa.
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi