Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Attahiru Ahmad, ya bada hakuri ga Hukumar Tsaron Sojojin Sama, dangane da zargin kashe fararen hula da aka yi wa sojojin a lokutan da suka kai hare-hare wasu yanzu.
Shugaban Majalisar Sarakunan, wanda kuma shi ne Sarkin Anka, ya bada wannan hakurin a lokacin da tawagar mutane bakwai da suka je binciken gano gaskiyar lamarin suka kai masa ziyara a Fadar sa a yau Lahadi a garin Anka, Jihar Zamfara.
Sarakunan Zamfara sun yi wannan zargi a cikin wata takardar da Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru ya yi a gaban manema labarai.
Wannan zargi da sarakuna suka yi ya biyo bayan wani zargi da Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali ya yi cewa wasu sarakuna na da hannu a kashe-kashen Zamfara.
Sarakunan sun fusata suka nemi ministan da ya fallasa wanda duk ya san ya na da hannu.
Shi kuma minista ya kalubalance su da su bayyana farar hular da aka kashe.
Wannan ne ya kai ga taron manema labarai da Sarkin Bubgudu ya gudanar har ya bayyana sunayen wadanda ya ce ann kashe, kuma aka jikkata da dama.
Wannan ya kai ga kafa kwamitin tantancewa daga Hafsan Hafsojin Saman Najeriya, Saddique Abubakar, wadda tuni tun ranar Juma’a ta dira Zamfara.
Sai dai kuma Sarkin Anka ya bada hakurin cewa taron manema labaran da aka yi, ba an yi ba ne don a ci zarafin sojojin sama.
Ya ce sun gudanar da taron ne gaba gadi saboda kalubalantar Ministan Tsaro, kuma wanda dan su ne, wanda ya yi musu mummunan zaton wai su na goya wa mahara baya.
“Ina ba ku hakuri dangane da rashin kyautawar da a ku ji a jikin su an yi muku. Irin haka ba za ta sake faruwa ba.”
Daga nan ya bada shawarar yadda za a rika fatattakar mahara daga sama, daga kasa kuma sojoji su rika bin su sun a riktsa su.
Ya kuma ce Sarkin Bungudu ya gudanar da taron manema labarai har ya bayyyana sunayen da ya ce an kashe ba tare da sanin shi Sarkin Anka ba.
“Sau hudu kawai muka san an taba kai hare-hare a bisa kuskure kan fararen hula, shi ma da dadewa can baya. Amma nan da watanni shida babu inda aka kai wa hari aka kashe mutane a bisa kuskure.”
A gefe daya kuma, Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya gwasale Sarakunan Jihar Zamfara, ya na cewa duk wadanda sarakunan suka ce an kashe, ba fararen hula ba ne, duk mahara ne.
Yari ya ce Gwamnatin Zamfara ba za ta yi da-na-sani ko bada hakuri ba dangane da wadanda aka kashe a Dumburum, cikin Karamar Hukumar Zurmi.
Ya ce kauyen ya yi kaurin suna wajen boye maharan da ke kashe mutane tare da yin garkuwa da banka wa kauyuka wuta a Karamar Hukuamr Zurmi.
Ya yi wannan jawabi ne ga tawagar bincike a lokacin da ta ziyarce shi a gidan sa da ke Talata Mafara, Jihar Zamfara.