Jarumi Adam Zango ya garzaya garin Gwandu ranar Juma’a duk da shela da yayi karara cewa ya dage auren sai bayan Sallah.
Babu wanda ya san dalilin da ya sa Zango ya sanar da dage daurin auren da ya dade yana shelar zai yi amma kuma kawai sai ga shi ya lillika hotunan daurin auren a shafin sa ta Instagram yana nuna shi a wajen daurin auren.
Sai dai kuma ba a ga wulkawan abokanan sana’ar sa ba a wurin daurin auren.
Ana ganin Zango ya yi haka ne saboda baya son mutane su halarci wannan daurin aure nasa, kamar yadda masu sharhi suka ce.
Wani makusancin Zango ya bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa ba a son kowa ya san cewa wai ga ainihin ranar da za a daura auren ne duk da cewa kuwa da kan sa Zango ne ya yi shelar auren sannan ya fito da kan sa ya ce babu auren.
Mutane da dama sun yi wa jarumi fatan alkhairi da zaman lafiya.
Wannan aure dai itace ta shida da Zango zai yi.