Wata mata mai suna Kafila, ta shaida wa Alkalin Kotun Gargajiya ta Idi-Ogungun da ke Agodi, Ibadan, Jihar Oyo cewa idan kotun ba ta auren ta da Lasisi Mukaila ba, to za ta kashe kan ta.
Za yi ikirarinn ba ta amfana da komai a zaman auren da ta ke yi da Mukaila sai yawan jibgar ta kawai da ya ke yi kamar jaka.
Mai Shari’a Mukalila Balogun ya zartas da cewa shaidun da ke gaban sa sun tabbatar da cewa mijin Kafila ya na yawan lakada mata dukan tsiya, kuma babu kulawa daga bangaren sa zuwa gare ta.
Ya ci gaba da cewa kotu ba ta jin dadi kuma ba ta murna da kashe aure a tsakanin ma’aurata. Amma kuma ba za ta zuba ido haka kawai ta bari wani mummunan al’amari ya faru ba.
Duk da mijin ta ya roki kotu kada a kashe masa aure, Mai Shari’a ya nuna masa cewa babu wata mafita sai an kashe auren, domin a ceci ran matar sa, wadda ta yi alkawarin za ta kashe kan ta idan ba a raba auren ba.
Amma kuma ya amince cewa ya na dukan ta. Sai dai ya yi wa kotu alkawarin zai canja halin sa.
“ Bayanan da matar ka ta yi sun nuna cewa ta ce ta gaji da zaman aure da kai, saboda azabtar da ita da ka ke yi. damac kuma ita ce ta amince za ta aure ka, yanzu kuma ta ce ta gaji.
“Saboda haka daga yamzun nan wannan kotu ta kashe aure tsakanin wadda ta yi kara da wanda ta yi kara. Dan da ku ka haifa zai kasance a hannun wadda ta shigar da kasa.
“ Wanda ake kara zai rika ba ta kudin ciyar da yaron da kuma kula da shi, naira 4,000 a kowane wata. Sannan kuma kada wanda ya kara tsokanar kowa da wata rigima.”