ZAMFARA: Sojojin sama sun kashe mahara da dama

0

Sojojin Saman Najeriya masu yin sintirin Operation Diran Mikiya, sun samu nasarar ratattaka mahara masu dimbin yawa a wani babban sansanin su da ke Ajiya, cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

Daraktan Yada Labarai na Hukumar Sojojin Sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana a cikin wata takardar karin bayani da ya fitar ga manema labarai a Abuja.

Ya ce an kashe mutane da dama a dazukan cikin kauyukan Ajiya da Wonaka cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji a Zamfara.

Ya ce an samu nasarar ragargaza maharan bayan da aka samu rahoto sahihi daga wani mutum cewa mahara su na tanadar muggan makamai da kuma abinci a cikin wani gida.

“Nan da nan mu ka tura zarata a cikin jirgin yaki samfurin Alpha Jet, tare da masu leken asiri da zarata, su ka kai wa wurin hari. An kai wa gidan hari ta sama, kuma a take ya kama da wuta, yadda har mahara da dama suka kone a cikin gidan.”

Ibikunle ya ce sojoji sun rika bin wadanda suka tsira a guje suna bindigewa. Hatta wadanda su ka tsere har zuwa Wonaka duk an bi su an bindige su.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ci karo da wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya (Ba mu tabbacin gaskiyar wannan bidiyo) a yau Lahadi inda aka nuno tulin gawarwakin maharan da sojoji su ka kashe, an shanya su a kan titin shiga cikin wani barikin sojoji.

Gawarwakin wadanda akalla za su kai 50, da yawan su babu kai, wasu babu kafafu, wasu a kone, wasu kuma babu hannaye.

Za a iya cewa sun fi kama da gawarwakin da aka kashe ta hanyar jefa bam.

Sannan kuma za a rika jin muryar sojoji su na bayyana yadda su ka kashe su.

Cikin kafafen soshiyal midiya da suka watsa bidiyon, har da Scannews.

Share.

game da Author