Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta fara atisayin ‘Operation Tsaftan Daji’ domin fatattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso Yammacin Najeriya.
Jami’in rundunar Napoleon Bali ya sanar da haka a garin Katsina ranar Talata.
” Kowa ya san yadda gwamnatin Najeriya ta maida hankali wajen ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a dazukan wannan yanki na Arewa Maso Yamma, amma wadannan miyagun mutane na neman su maido wa gwamnati da hannun agogo baya. A dalilin haka ne rundunar sojin sama ta fito domin a fafafata da ita wajen ganin an fatattaki wadannan muggan iri a kasar nan.
” Za mu yi amfani da jiragen mu na sama domin fara wa irin wadannan miyagun mutane da kuma ruguza maboyan su a dazukan.
Bali y ace rundunar za ta fi maida hankali ne a dazukan dake jihar Zamfara da wadanda ke kusa da jihar.
Ya kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da samar wa rundunar bayanai masu amfani domin samun nasara a aikin da suka sa a gaba.
” Mun tanaji manyan jirage masu aman wuta ta ko-ina da kuma wasu zaratan makamai domin ganin mun ragargaza wadannan yan ta’adda a wadannan dazuka.
Discussion about this post