ZAMFARA: Ana samun karuwar yara dake fama da matsalolin shakar iska mai guba – MSF

0

Kungiyar likitocin jinkai Médecins Sans Frontières (MSF) ya bayyana cewa har yanzu suna na kula da yara sama da 150 dake fama da matsalar shakar gubar iskar hakin ma’adinai da ake yi a Jihar Zamfara.

Jami’in kungiyar Simba Tirima ya fadi haka da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.

Bayanai sun nuna cewa cutar ya kan kama yara kanana ne a mafi yawan lokutta. Kuma yakan hana su girma yadda ya kamata da hana kaifin kwakwalwa.

Alamun kamuwa da wannan cuta sun hada da yawan fama da ciwon ciki, ciwon kai, mantuwa, rashin haihuwa da makamantan su.

An yi kira da a rika zuwa asibiti da zaran ba a ji daidai ba a jiki sannan a nisanta yara daga kusanta da inda ake gine-gine da hake-hake.

Tirima ya ce idan ba a manta ba a 2010 irin wannan iskar kura mai guba ya yi ajalin yara 400 a jihar Zamfara sannan a 2015 irin haka ya yi ajalin yara 30 a jihar Neja.

Ya kuma kara da cewa a Yanzu haka MSF na kula da yara 150 da suka kamu da wannan cuta a jihar Zamfara duk da fama da suke yi da ayyukan mahara a wannan jiha.

Share.

game da Author