ZAMFARA: A dora laifin kashe-kashe kan Ministan Tsaro, ba a kan Gwamna Yari ba -Kungiya

0

Wata Kungiyar Sa Kan Neman ’Yancin Jama’a, mai suna PAIR, ta dora alhakin mummunan kashe-kashen da ake yi a Jihar Zamfara a kan Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali, maimakon Gwamna Abdul’aziz Yari.

Ba PAIR ce kadai ta dara wa Minista Dan Ali wannan alhakin ba, har da Kungiyar SGE, NEO da TPC, dukkan su kungiyoyi ne na kwatar wa marasa karfi ’yanci, kuma sun ce Minsitan Tsaro ba shi yin wani gagarimin hobbasan da za a gani har a yaba cewa da gaske ya ke yi wajen ganin an magance fitinar.

Gamayyar Kungiyoyin sun ce Yari ya yiniyakar kokarin da dokar kasa ta wajabta masa, ta hanyar bayar da taimakon kayan aiki, sadarwa da bayanai, bayar da gidaje da kuma alawus na musamman ga ‘yan sanda da sojojin da aka tura a Zamafara, ba tare da wani samun taimako daga Ma’aikatar Tsaro ba.

A cikin wata sanarwa da Isa Yaro ya sa wa hannu, a madadin Gamayyar Kungiyoyin, a jiya Lahadi a Abuja, ya nuna rashin jin dadin yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa shawo kan wannan fitina a Jihar Zamfara sama da shekara biyu.

Isa ya ce tun tuni ya kamata a ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali.

“Me ya sa za a yi ta dora laifi ga Gwamna Yari, alhali shi gwamna ne kawai, ba shi ke da iko a kan ‘yan sanda da sojoji ba. da dadewa Yari ya sha jan hankalin gwamnatin tarayya game da yadda ake ta jigilar makamai zuwa jihar Zamfara, amma wadanda ya kamata su dakile abin daga tarayya ba su yi komai ba.

“Mu abin da mu ke son sani shi ne, wane irin kokari Ministan Tsaro, wanda dan Jihar Zamfara ne ya yi da za a iya jinjina masa wajen shawo kan kashe-kashe a Jihar Zamfara?

Yaro ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karatun ta-natsu, ya san irin mutanen da zai nada kan mukamai idan an shiga sabon zangon mulki na biyu a ranar 29 Ga Mayu.

Share.

game da Author