ZABEN SHUGABAN KASA: ‘Sace min kuri’u aka yi’ – Moghalu

0

Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar YPP, Victor Moghalu, ya jaddada cewa an sace masa kurri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar acrnar 23 Ga Fabrairu.

Da ya ke tattaunawa da mujallar The Interview a Abuja, Maghalu ya ce ya na da tulin hujjojin da ke tabbatar da cewa an yi masa magudi, an karkatar masa da kuri’u, kuma sace masa tulin kuri’u.

Ya kara shaida wa mujallar cewa wadanda na su kaunar ci gaban kasar nan ne daga kyawawan manufofin da ya bijiro da su, ne suka rika yi masa makarkashiya, ta hanyar yayata labarai na karya da karairayi a kan sa.

Moghalu ya kuma nanata cewa shi kadai ne dan takarar da aka yi wa wannan sharrin.

Ya ce kwanaki biyu kafin zabe an rika yayata cewa wai ya janye wa manyan ‘yan takarar shugabancin kasar nan biyu.

Moghalu ya ce wannan ji-ta-ji-ta ta kashe guyawun magoya bayan sa da yawan gaske, ta yadda ba su fita jefa kuri’a ba.

Dan takatar ya ce duk abin da aka rika yayatawa dangane da shi, sai ya kasance an yarda a Arewacin kasar nan inda magoya bayan Buhari ke da yawa, da kuma kudancin kasar nan inda na Atiku ke da yawa shi ma.

Sai dai kuma ya ce duk da wannan rashin mutunci a siyasa da aka yi masa, ba zai kalubalanci sakamakon zaben ba.

Amma dai ya ce da a ce ma shi ne ya zo na biyu, to da akwai dan dama-dama.

Daga nan sai ya ce abin da zai fi maida hankali a yanzu shi ne kamfen din ganin an kawo sauyi a tsarin zabe, ta hanyar shimfida sabon tsari wanda sabbin dokokin zabe za su bijiro da shi.

A karshe ya ce ya gamsu zaben da aka gudanar ya karkata ne ga inda tunanin jama’a ya fi karkata.

Share.

game da Author