Ya zuwa yanzu dai akwai kararrakin korafe-korafen zaben 2019 har guda 766 wadanda ke a gaban kotunan sauraren kararrakin zabe.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Rajistara ta Kotun Dukaka Kararrakin Zabe, Rabi Abdulazeez ta aiko wa PREMIUM TIMES, ta ce wadannan adadin kararrakin da aka shigar ne zuwa 16 Ga Afrilu tukunna.
Rabi ta ce Shugabar Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa ta kafa kotunan sauraren kararrakin da suka shafi zaben 2019 har guda 77.
Har zuwa yanzu dai kararrakin da aka shigar dangane da zaben shugaban kasa guda hudu ne kadai.
Yayin da kararrakin zaben Majalisar Tarayya 101 ne, na zaben Majalisar Dattawa kuwa 207 ne.
An shigar da kararrakin zaben gwamna guda 54, na Majalisar Dokokin Jihohi kuma 402.
’Yan takarar shugaban kasa hudu ne su ka garzaya kotu su ka kalubalanci nasarar da INEC ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben na 23 Fabrairu, 2019.
Jam’iyyun da ke kalubalantar zaben shugaban kasa, sun hada da PDP, HDP sai kuma PDM da CC.
Dukkan jam’iyyun hudu sun hada APC, Buhari da INEC sun maka kotu. Sai dai ita CC har da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ta hada, duk ta maka kotu.
Discussion about this post