Shugaban sashen aiyukkan gona da dabbobi na ma’aikatan Gona a jihar Jigawa Kabiru Haruna ya bayyana cewa gwamnati za ta yi wa dabobbi 21,300 allurar rigakafi ‘bovine pleuropneumonia (CBP) da pests des petits ruminants (PPR)’ domin dakile yaduwar cututtukan dake kama dabobi a jihar.
Haruna ya sanar da haka wa manema labarai ranar Litini a garin Guri.
Ya kara da cewa gwamnati zata yi haka ne domin ingantan kiwon lafiyar dabobbi da kuma samar da nama da madara masu tsafta ga mutane.
” Za a yi wa shanu 10,000, awakai da tumakai 11,000 sannan kuma da karnuka 300.
Haruna ya ce a dalilin haka gwamnati ke kira ga duk masu dabobbi da su gaggauta kai dabobbin su asibitin dabobbi mafi kusa da su domin yi musu wannan allura na rigakafi.
A karshe sakataren kungiyar makiyaya na Miyetti Allah reshen jihar jihar Jigawa, Ado Bodallah ya yabawa gwamnati bisa wannan kokari da ta yi na ganin an tsaftace dabbobi a jihar. Sannan kuma yayi kira ga makiyaya da su tabbata sun mika dabbobin su domin yi musu rigakafi cewa duk wanda bai yi haka ba toh zai fuskanci horo.
Discussion about this post