Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta bayyana cewa yunkuri ko niyyar da Aisha Buhari ta ce ke yi da nufin gina Jami’ar Muhammadu Buhari, bai yi daidai da tsarin ilmi a kasar nan, kuma abin ya wuce barkwanci, sai dai su kira shi rainin hankali.
Shugaban ASUU Reshen Jami’ar Ibadan, Deji Omole ne ya yi wannan kalami jiya Talata, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Ya na martani ne a kan furucin da Aisha Buhari ta yi cewa akwai shiri na nan na kafa Jami’ar Muhammadu Buhari.
Haka dai ta fada da bakin ta a wani taro a Yola, jihar Adamawa a ranar Asabar da ta gabata, inda ta ce za a saka wa jami’ar suna “Muhammadu Buhari University”.
Shi kuwa Omole a na sa martanin, cewa ya yi kokarin kafa wannan jami’a ya tabbatar da dalilin da ya sa Buhari ke ci gaba da rage kasafin kudin da ya ke kashewa wajen inganta ilmi a kasar nan a kowace shekara.
Shugaban na ASSU ya ce tunda Buhari ya h au mulki a duk shekara sai ya zabtare yawan kasafin kudin fannin ilmi.
“Ni da na ji cewa ana kokarin gina jami’a mai zaman kanta da za a sa mata sunan Buhari, na dauki abin rainin hankali kawai.
“Idan dai har mu na da shugaban kasa wanda ke ci gaba da rage kudaden da ya ke kashewa a fannin ilmin kasar sa, sannan kuma a ce iyalan sa za su gina jami’a tare da hadin guiwar ‘yan kasashen waje, Ina tunanin abin zai zama bala’i ga tsarin ilmi da ci gaban sa a kasar nan da kuma abin kunya ga shi shugaban kasa.
“Hakan na nuni da cewa ‘yan Najeriya su sani wannan shugaban bai yi amanna da ingancin ilmin makarantun gwamnati ba kenan, ballantana ya kara karfafa su.”
Shi kuwa Ma’ajin Kungiyar ASSU, cewa ya yi Aisha Buhari ta dakata tukunna har sai mijin ta ya sauka daga mulki, sai ta gina duk ma abin da ta ke so ta gina.
Haka Ma’ajin ASSU, Ademola Aremu ya bayyana.