Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta bada sanarwar cafke batagari 36 a cikin ‘yan makonni kadan tare da kwato shanun da barayin shanu suka sace har 486.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya bayyana wa manema labarai haka a jiya Juma’a a Kaduna.
Ya danganta wannan nasara da kaddamar da gagarimin shirin tsaro na Operation Puff Adder, wanda Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kaddamar.
Karkashin wannan shiri dai an karfafa matakan tsaro sosai a kan titin Kaduna zuwa Abuja, inda cikin wannan shekara garkuwa da mutane ta kara muni a kan titin.
Ya ce an kuma samu damke batagari a wurare daban-masu wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar.
Kwamishinan ya kara da bayanin cewa an kwato shanu 393, tumaki 93 daga hannun barayin shanu.
Daga cikin batagarin da aka kama kuwa, an samu tara da hada hannu da masu fashi da makami, 18 kuma garkuwa da mutane, shida kuma masu satar shanu.
Ya ce akasarin su masu shekaru 20 ne zuwa 30, kuma za a gurfanar da su kotu.
Discussion about this post