Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bada sanarwar cafke wasu mutane su uku da ta ke zargin su da hannu wajen yin garkuwa da dan jaridar da ke aiki a Gidan Talbijin na Channels, a Abuja.
Wadanda ake zargin sun gudu da Friday Okeregbe, wanda dan rahoto ne a gidan talbijin na Channels, amma suka sake shi a ranar 28 Ga Maris, bayan ya shafe kwanaki shida a hannun su.
Wadanda aka kama din sun hada da Hanniel Patrick, Abdulwahab Isah da Salisu Mohammed.
Sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa, Frank Mba ya bayar, ta ce an kama wadanda ake zargin tun a ranar 9 Ga Afrilu. Ya ce jami’an ‘Operation Puff Adder’ ne suka damke su.
Ya ce sun kama Okeregbe, wanda ba shi ne suka yi niyyar damkewa ba da farko. Sun boye shi a wata mabuyar masu garkuwa da mutane a garin Karmo da ke gefen Abuja.
Mba ya ce an samu bindiga samfurin libarba ta gargajiya, harsashen bindiga AK 47 uku, gatari, wayoyin hannu, hulunan rufe wa wadanda suka kama fuska da sauran kayayyaki a hannun su.
Ya ce ana kokarin kamo sauran wadanda su ka rage din. Kuma da an kammala bincike za a gurfanar da su a kotu.