‘Yan sandan Jihar Edo sun bada nasarwar damke wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne, kuma ya yi ikirarin ya kashe mutane 38.
Sanarwar da kakakin yada labaran su na jihar, Chidi Nwabuzor ya bayar, ya ce an kama wanda ake zargin ranar Talatar da ta gabata, bayan samun wasu sahihan bayanai na sirri dangane da mutumin.
Nwabuzor ya ce an damke mutumin ne mai shekaru 37 a lokacin da ya ke shirin kashe wasu mutane da ya tsara kashewa daya bayan daya.
Sun ce ba za su bayyana sunayen mutanen da ya yi shirin kashewa din ba.
Ya kara da cewa, bayan an damke mutumin, an kuma bincike shi aka same shi da bindigogi har guda biyu.
Nan da nan bayan kama shi, an tsare a bangaren CID, aka yi masa tambayoyi, har ya yi bayanin cewa da hannun sa ya kashe mutane 38.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Edo, Mohammed Danmalam ya ce ana ci gaba da bincike, daga nan kuma kotu ta yi aikin ta na hukunta duk wanda aka kama da laifi.
Yayi kira jam’a su rika kaffa-kaffa, kuma su ci gaba cda gudanar da harkokin su lami lafiya.
Discussion about this post