Jiya Litinin ne wasu ’yan fashi da makami suka kai farmaki a wani banki da ke garin Ido-Ani, cikink Karamar Hukumar Ose, a Jihar Ondo, inda a harin har suka kashe mutane bakwai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai farmakin ne wajen karfe 2 na rana, a bankin da ke cikin unguwar Isewa.
PEMIUM TIMES ta samu tabbatacin cewa wadanda aka bindige a bankin sun hada da ma’aikatan bankin su biyar, shugaban wata makarantar sakandare da kuma da kuma wani dan sanda daya.
An kuma hakkake cewa masu fashin sun gudu da makudan kudaden da ba a san takamaimen adadin sub a.
Wadanda suka gane wa idon su lokacin da abin ya faru, sun ce sai da ‘yan fashin suka shafe awa daya kafin su fice daga bankin.
Dama kuma lokacinn da suka isa bankin, sun rika harba bindigogi a sama, daga nan suka darkaki bankin bayan sun sa nakiya sun dagargaza kofar shiga cikin bankin.
Ko kafin sojojin da ke Barikin Isua Akoko da kuma ‘yan sandan cikin garin su kai dauki, tuni masu fashin sun arce da kudaden da suka kwashe.
Baya ga wadanda suka mutu, wasu da dama sun samu raunuka daga harbin bindiga, inda a halin yanzu su na asibitin Owo da na Ido-Ani ana kula da su.
Kakakin Yada Labarai na ’Yan sandan jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar fashin.
Ya tabbatar da cewa an kama daya daga cikin ’yan fashin, kuma ana ci gaba da kwakkwaran binciken yadda za a kamo sauran.