Yadda zaben 2019 ya kwance wa mata zani a kasuwa

0

Bincike ya nuna cewa tun bayan dawowa mulkin Dimokradiyya a Najeriya, zaben 2019 shi ne wanda ya zama mafi koma baya ga mata a Najeriya.

Dalili, na farko dai yawan masu mukamai na siyasa ba su karu ba, bayan zaben 2019. Maimakon haka, sai ma raguwa aka samu bayan an kammala zabuka.

Tun daga jamhuriya ta hudu ake ta samun raguwar mata madafun iko da mayan mukamai na siyasa ko nasarar zabuka.

Jaridar PREMIUM TIMES ce tare da hadin kan Cibiyar CCD ne suka tabbatar da gaskiyar wannan nazari da suka gudanar.

YAUSHE ZA A BAI WA MATA CIKAKKAR DAMA CIKIN GWAMNATI?

An jima ana hankoron ganin an kara bai wa mata gurabun da za su kara cikewa a cikin gwamnati, tun kafin zaben 2019.

An rika hasashen cewa tunda an kafa jam’iyyu har 91, to wannan karo za a dama da mata sosai a cikin gwamnati.

Ganin yawan wadanda suka fito takarar zabukan fidda gwani, sai aka kara sa dai cewa to mata fa sun yunkuro a wannan zaben.

KWAN-GABA-KWAN-BAYA….

Wata kididdiga da CCD ta fito da ita, ta nuna cewa an zubar da mata masu yawan gaske tun ma a zabukan fidda-gwani.

Sannan kuma gaba daya mata 62 kadai aka zaba a mukamai daban-daban a zaben 2019, a fadin kasar nan.

Wannan ya nuna cewa kashi 4.17 bisa 100 ne kadai mata daga cikin ‘yan takarar da aka zaba a 2019.

Kenan an samu raguwa daga adadin kashi 5.65 da suka ci zabe a 2015.

Bincike na can baya kuma ya tabbatar da cewa tun daga lokacin kafa dimokradiyya a Najeriya har zuwa yau, ba a taba samun zangon siyasar da mata suka fito takara ba har aka zabi kashi 10 bisa 100 na ‘yan takara mata.

YADDA ZABEN 2019 YA KWANCE WA MATA ZANI

Kididdiga ta nuna mata na da kaso 49.4 daga cikin kashi 100 na al’ummar Najeriya. Bayanai daga Hukumar Kididdigar Alkaluma ta Kasa (NBS) suka tabbatar da haka.

Sai dai kuma duk da wannan yawa na su kusan rabin al’ummar Najeriya, mata 2,970 cif suka fito takarar mukamai daban-daban a zaben 2019.

Wannan adadi kuwa shi ne kashi 11.36 bisa 100 na jimlar ’yan takarar mukamai daban-daban a zaben 2019. Wato kashi 88.64 bisa 100 na masu takara duk maza ne.

KARAMBANIN TSAYAWA TAKARAR SHUGABANCIN KASA

Mutane da yawa sun tafi a kan cewa hakikanin gaskiya mata ko kusa basu shirya neman shugabancin kasar nan ba. Abubuwan da suka rika faruwa ana saura kwanaki kadan a yi zabe sun tabbatar da haka.

Mata shida masu takarar shugabancin kasa sun janye takarar su, kwanaki kadan kafin zabe. Amma kuma sunan sun a kan kuri’un zabe, INEC ba ta cire sunayen su ba, saboda sun janye a kurarren lokacin da ba a iya cire sunayen su da jam’iyyar su.

Cikin wadanda suka janye har da Obiagelli Ezekwesili, wadda ake ganin ta na da kazar-kazar da himma sosai.

KO DAI WUTSIYAR RAKUMI TA YI NISA DA KASA?

Rabon da a samu mata a masu yawa a Majalisar Tarayya, tun zaben 1999, inda aka samu mata sanatoci 3, Mambobin Majalisar Tarayya 12, wato su 15 kenan kacal, a cikin sanatoci 109 da mambobi 340.

MATA A TAKARAR MAJALISA A 2019

A zaben 2019, mata 235 sun fito takarar zaben fidda-gwani na majalisa, amma 7 suka ci zaben fidda gwani a APC, 10 kuma suka fito daga PDP.

A cikin 17 din, Binta Masi Garba, ba ta samu yin nasara karo na biyu ba, an kayar da ita. Haka ita ma Shugabar Marasa Rinjaye Abiodun Olujimi, ta rasa kujerar ta.

Mata 533 suka nemi takarar Majalisar Tarayya, inda APC ta na da 15, ita kuma PDP na da masu takara mata 16.

BABU GWAMNA MACE

A matakin Jiha kuwa, har yau babu gwamna mace. Kashi 3.07 kadai suka nemi takara, kuma duk sun fadi.

Mata 275 ne kadai suka fito takara a mataimakin gwamna, amma 4 sun yi nasara a jihohin Enugu, Kaduna, Ogun da Rivers, duk sun yi nasara.

Kenan shi ma adadin mata mataimakan gwamna ya ragu kenan daga 6 a zaben 2015 zuwa 4 a zaben 2019.

A 2019 an zabi mata 4o a majalisar dokokin ta jihohi daban-daban. Wannan ya nuna an samu raguwa matuka, domin a zaben 2015 an samu mata 55 a majalisar dokoki ta jihohi daban-daban.

DALILAI

Wasu daga cikin dalilan da aka rika bayarwa akwai rashin bayar da dama ga ma su shiga a dama da su a cikin siyasa.

Akwai kuma yanayin yadda salon siyasar ya juya, ta yadda aka kafa saka tsoro, fargaba ta hanyar tashe-tashen hankula da rikice-rikice a lokacin kamfen da zabubbuka.

Akwai kuma yadda ake tafka magudi tare da harkallar cuwa-cuwa da cinikin kuri’u.

Kola Olabandiyan kakakin jam’iyyar PDP na daga cikin wadanda suka bada wannan dalili na sama.

“Duk da haka jam’iyyar PDP ta bai wa mata dama fiye da sauran jam’iyyu, domin PDP ta fi yawan matan da suka samu nasara a zabuka daban-daban.

Daga cikin mata 62 da aka zaba a mukamai daban-daban, PDP na da 33, APC na da 23.

Share.

game da Author