Yadda wasu mahara suka guntile wa Habibu hannayen sa biyu a Sokoto

0

A ranar Lahadin da ya gabata ne da wajen misalin karfe biyun dare a garin Mana dake jihar Sokoto wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka far wa wani dalibin jami’ar Usmanu Dan Fodio mai suna Habibu Abubakar inda suka guntile masa duka hannayen sa bibiyu sannan suka tafi da babur din sa.

Mahaifin Habibu, Abubakar Attahiru ne ya sanar wa ‘Daily Nigerian’ haka ranar Litini.

Attahiru yace Habibu na nan kwance a babban asibitin Wamakko ana duba shi, sannan kuma har ziwa yanzu ba a iya kamo wadanda suka aikata haka ga Habibu ba.

Wani abokin karatun Habibu mai suna Haruna ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Habibu mutum ne da babu ruwan sa a shiga harkar da bai shafe sa ba kuma hakan ya ba muatane mamaki matuka bayan jin abin da aka yi masa.

” Habibu shine moniton ajinmu sannan duk iya matsi Habibu ba zai tankaka ba ballantana ya yi fushi.

A karshe wani ma’aikaci a jami’ar Danfodio din ya ce wannan tsautsayi da ya fada wa Habibu ba a cikin makarantar ya auku da shi ba.
Amma kuma hukumomin jami’ar sun ce za su bi diddigin abin da ya faru.

Share.

game da Author