Yadda ‘Tramol da Kodin suka halaka daliban jami’a su uku

0

An samu wasu daliban Jami’ar Fasaha ta Owerri da ke Jihar Imo, su uku a mace a dakin otal din su, bayan sun garwaya kwayoyin kodin da ruwan maganin taramol sun nuske.

An kuma tabbatar da cewa har ma da ruwan barasar nan mai karfin bugarwa mai suna Vodka suka hada su ka sha, kafin mutuwar ta riske su a buge.

An samu dalibi na hudu a buge, kuma a sume, inda aka garzaya da shi asibiti, domin a ceci ran sa.

An samu gawarwakin daliban ne a gidan kwanan dalibai na Sunshine Castle Hostel, Umuchima, da ke kusa da jami’ar da su ke karatu.

Wani ganau ya shaida cewa biyu daga cikin mamatan a nan take suka mutu, yayin da daya daga cikin matan dak suke tare da kuma wani namiji, su kuma an same su kwance sumammu, ba su san inda su ke ba.

An garzaya da su asibitin Gwamnatin Tarayya na Owerri, inda aka kwantar da su a bangaren kula da wadanda ke kan gargarar mutuwa.

Bayan an kwantar da su ne namiji daya ya mutu, duk da cewa likitoci sun yi iyakar kokarin ganin sun ceci ransa, amma ba su yi nasara ba.

Wannan al’amari da ya faru ya sa daliban da ke cikin gidan dukkan su sun gudu daga gidan, yayin da ’yan sanda suka damke mai kula da gidan kwanan daliban.

Kakakin jami’ar, Uche Nwaelue, ya ce har zuwa yanzu ba su kai ga tantance ko mamatan daliban jami’ar ba ne ko ba su ba ne.

Shi kuma kakakin ‘yan sanda Orlando Ikeokwu, ya ce sun samu labarin ne da rahoton mai kula da gidan, inda daga nan su ka garzaya, kuma suka same su su hudu a tsirara, kuma sumammu.

Ya ce sun garzaya da su asibiti, inda aka tabbatar musu da mutuwar uku daga cikin su.

Ikeokwu ya ce an samu taramol da tabar wiwi a tare da su.

Share.

game da Author