Mai mallakin fitaccen gidan abinci dake Abuja, Shagalinku ya bayyana cewa akaron farko ya fadawa masu garkuwa a titin Abuja zuwa Kaduna.
A ranar Litinin ne masu garkuwa suka tare titin Abuja zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane dama ciki har da shugaban hukumar UBEC ta kasa Mohammed Mahmood tare da ‘yar sa.
Kamfanin dillancin labaran Nageriya ta ruwaito cewa ba a ranar Litinin ba, maharan sun tare wannan hanya ma a ranar Lahadi inda suka yi garkuwa da mutane.
Umar Shagalinku ya shaida wa NAN cewa bai taba cin karo da masu garkuwa da mutane a wannan hanya ba sai ranar litini.
Ya ce shi dai yakan ji ana fadi ne cewa ana sace-sacen mutane a wannan hanya kawai sai gashi ya kuskure su.
Wakilin jaridar NAN ya kara da cewa shima Allah ne ya kiyaye da ya fada musu.
Har yanzu dai wannan abin tashin hankali yaki ci yaki cinyewa a wannan titi duk da sanarwan da ‘yan sanda ciki har da sufeto Janar na Kasa wai sun kakkabe maharan da suka addabi matafiya a wannan hanya.