Yadda Jam’iyyar APC ya kamata ta raba mukamai a Majalisar Tarayya, Daga Kais Daud Sallau

0

A duk lokacin da akayi zabe aka gama, jam’iyar da ta samu nasara tana kasa mukamai musamman ta yadda suka fi samun goyon baya lokacin zabe.
Ta yadda kowace yanki zata ji anyi da ita a gwamnati kamar yadda muka saba gani.

A Najeriya muna da shiyoyi na siyasa guda shida (SIX GEOPOLITICAL ZONES) sun hada da;

Arewa ta tsakiya (North Central)
Arewa maso gabas (North East)
Arewa maso yamma (North West)
Kudu maso gabas (South East)
Kudu maso kudu (South South)
Kudu maso yamma (South West)

AREWA MASO TSAKIYA (NORTH CENTRAL) Akwai

Benue, Kwara, Kogi, Nasarawa, Plateau, Niger, da Federal Capital Territory (FCT)

Arewa ta tsakiya itace yankin da tunda muka dawo mulkin farin hulla daga (1999) har zuwa yanzun basu taba samun wata mukami mai gwabi a majalisar wakilai ta kasa ba. Saboda haka Arewa ta Tsakiya sun cancanci a basu dama su kawo shugaban majalisar wakilai (SPEAKER), ta yadda suma zasu ji anyi da su na kuri’u kashi saba’in cikin dari (70%) da suka kawo jam’iyar APC.

AREWA MASO GABAS (NORTH EAST) Akwai

Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, Yobe

Arewa maso gabas ta na daya daga cikin yankunan da suka dandazowa jam’iyar APC kuri’u a zabe da ta gabata. Ya kamata suma a wannan lokacin a basu dama su kawo shugaban majalisar dattijai (SENATE PRESIDENT) domin saka musu da goyon baya da suka yi har ya kai ga nasara jam’iyar APC kan mulki karo na biyu.

AREWA MASO YAMMA (NORTH WEST)

Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, Zamfara

Idan muka dauka arewa maso yamma, wannan yanki nan shugaban kasa MUHAMMADU BUHARI ya fito, saboda da haka sun samu tasu kasau, wacce ta fi ko wace kasau girma.

KUDU MASO GABAS (SOUTH EAST)

Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo

Kudu maso gabas tana daya daga cikin yankin da jam’iyar APC mai mulki bata samu kuri’un a zo a gani ba, kokuma mu ce itace yankin da ta ba APC mafi karancin kuri’a a zaben da ta gabata. Saboda haka duk matsayin da aka basu, basu da dalilin korafi sakamakon kin goyawa jam’iyar APC baya a zaben da ya gabata. Za’a iya basu mai tsawatarwa na majalisa (CHIEF WHIP) na majalisar dattijai ko na wakilai.

KUDU MASO KUDU (SOUTH SOUTH) Akwai

Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Rivers, Delta, Edo

Wannan yankin itace yankin da Shugaban jam’iyar APC ADAM OSHIOMHOLE ya fito, kuma sune yanki na biyu da jam’iyar APC ta fi samun kuri’u daga yankin kudu. Ya kamata a basu dama su kawo mataimakin shugaban majalisar dattijai (DEPUTY SENATE PRESIDENT), saboda wannan yanki sun ba jam’iyar APC goyon baya sabanin yadda suka saba yi a zabukan baya wanda suna daya daga cikin yankin da suke ba jam’iyar PDP kuri’u masu yawa a baya. Amma a wannan karon an samu canji kuri’u a yankin.

AREWA MASO YAMMA (SOUTH WEST)

Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun, Oyo

Arewa maso yamma shi ne yankin da mataimakin shugaban kasa PROF. YEMI OSINBAJO (SAN) ya fito, wanda wannan matsayin shi ne na biyu a Nigeriya. Saboda goyon bayan da suka ba jam’iyar APC a zaben da ya gabata, kuma sune yankin da suka baiwa jam’iyar APC kuri’un da yafi yawa daga yanki kudu. Saboda haka sun cancanci a kara musu da mataimakin shugaban majalisar wakilai (DEPUTY SPEAKER) domin suma sun dan taka rawan gani.

KIRA GA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI DA JAM’IYAR APC TA KASA

Ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da shuwagabannin jam’iyar APC da kada su bari gudun zuciya da son zuciya yasa a koma gidan jiya a majalisar dokoki. Bai kamata ace yankin da suke da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ace wai zasu sake rikici wai sai sun kawo shugaban majalisa na wakilai (SPEAKER) ko na dattijai (SENATE PRESIDENT) hakan ba adalci ba ne.

Ya kamata muyiwa junan mu adalci ta yadda kowa zai ji anyi da shi, mu cire son zuciya, muyi abinda ya dace, sai a tafi tare. Amma duk lokacin da aka ce son zuciya za’a sa a gaba, ba za’a raba mukamai ta yadda kowa zai samu ba, toh fa za’a iya maimaita irin abinda su BUKOLA SARAKI suka yi a majalisar. Domin rashin adalci da son zuciya shi yake kawo baraka.

Ina tare da Matakin Jam’iyar APC akan SEN. SEN. AHMED LAWAN da ya zama shugaban majalisar dattijai (SENATE PRESIDENT) kamar yadda APC ta zabe shi, amma a majalisa wakilai da suka kawo HON. FEMI GBAJABIAMILA bana tare da su, kuma bai dace ba a siyasance, ba adalci a nan, son zuciya ne, baza mu yarda ba, domin daga wannan yankin mataimakin shugaban kasa PROF. YEMI OSINBAJO ya fito, mukami na biyu a kasa.

Arewa ta tsakiya (North Central) su ya dace su kawo shugaban majalisar wakilai (SPEAKER) saboda a samu daidaito a guri kasa mukamai, domin kowa yaga irin kuri’un da mutanen Arewa ta tsakiya (North Central) suka baiwa jam’iyar APC, ya kamata a saka mu ta hanyar basu shugaban majalisar wakilai (SPEAKER).

Allah ya ba Wadanda aka Zaba Ikon yin Shugabanci Nagari. Allah ya ba mu Zaman Lafiya a Kasar Mu. Amen.

Share.

game da Author