Yadda aka haife ni a Najeriya, kuma na tashi a cikin ta –Atiku

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa cewa shi haifaffen Najeriya ne, don haka ya cancanta tsayawa takarar shugaban kasa.

Atiku ya aika wa kotu wannan ne a matsayin martani ga kukan da APC ta aika wa kotun a rubuce cewa ba cikin Atiku ba dan Najeriya ba ne, domin a lokacin da aka haife shi a Jada, ta na cikin kasar Kamaru ce kafin a maida ta cikin Najeriya.

PREMIUM TIMES ta mallaki kwafen hujjojin da Atiku ya damka a yau Litinin da safe.

Dokar Najeriya ta ce sai wanda aka haifa a Najeriya ne zai iya tsayawa takarar shugaban kasa.

Dokar ta fassara dan kasa wanda aka haifa a Najeriya cewa shi ne wanda aka haifa cikin Najeriya tun daga 1 Ga Janairu, 1960, ko kuma wanda iyayen sa a Najeriya aka haife su.

Atiku ya ce ya cika sharuddan fitowa takarar shugabancin kasa, saboda asalin kakan sa na wajen uba, Garba Atiku Abubakar, dan Jihar Sokoto ne, wanda aka haifa a Wurno, cikin Jihar Sokoto.

An haifi Atiku a Jada, wadda a lokacin da aka haife shi cikin 1946, ta na karkashin kasar Kamaru ce, kafin yarjejeyar Majalisar Dinkin Duniya ta Raba-Gardama (Referendum) ta maida yankin da al’ummar da ke cikin ta a bangaren Najeriya, bayan sun zabi zama Najeriya maimakon Kamaru.

Atiku ya ce kakan na sa na wajen uba, dan tireda ne daga Wurno ya zauna Jada, tare da abokin sa mai suna Ardo Usman.

Ya ce a Jada aka haifi mahaifin sa mai suna Garba.

Mahaifiyar Atiku kuwa mai suna Aisha Kande, ‘yar wani basarake ce daga Dutse, Jihar Jigawa. Ya ce iyayen sa duk Fulani ne, daya daga cikin kabilun Najeriya masu tarin yawa.

Share.

game da Author