Wike ya yi nasara a zaben Ribas

0

Malamin Zaben gwamna na jihar Ribas, Teddy Adias ya sanar da sakamakon zaben jihar Ribas inda ya bayyana cewa gwamna mai ci, Nyesom Wike na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben gwamnan jihar.

A sakamakon zaben da Adias ya karanta, gwamna Wike ya samu kuri’u 886,264 inda shi kuma Biokpomabo Awara na jam’iyyar AAC ya samu kuri’u 173,859.

Share.

game da Author