Wasu tubabbun mambobin Kungiyar Boko Haram sun roki ‘yan Najeriya da su yafe musu ayyukan barnar da suka tafka a baya.
Tubabbun sun bayyyana haka ne a lokacin da suke amsa tambayoyi daga wani wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najariya (NAN).
A jiya Laraba ne aka yi hirar da su bayan sun kammala shirin wanke musu kwakwalwa da tsarkake musu zzukata, domin karkato su daga Boko Haram tare da koya musu sana’o’in domin dogaro da kai.
An yi musu wannan horo ne a Sansanin NYSC da ke Malam-Sidi, cikin karkashin Karamar Hukumar Kwami, Jihar Gombe.
Wani mai suna Bappah Nura, ya ce a baya shi manomi ne, amma sai daga baya ya shiga Boko Haram a Jihar Barno.
Ya ce ribbatar sa aka yi da ya shiga Boko Haram, amma sai bayan ya shiga ya fahimci abin na su dauk karya ce kawai.
Daga nan sai y ace ya na da-na-sanin shiga Boko Harfam da yayi.
“Ina rokon ’yan Najeriya su yafe min. Na yi da-na-sanin shiga Boko Haram. Dama ribbata ta aka yi, ba da son rain a ba. A yafe min.” Inji Nura.
Ya ce a yau ya gode wa gwamnatin Muhammadu Buhari dangane da bayar da dama tura su kwas na tsarkake musu zukata tare da koya musu sana’o’in hannu da za su dogara da kan su.
Ya yi fatan zai koma garin su Bama, cike da alfaharin koyon sana’ar yin takalmi.
Ya ce yanzu shi jakada ne na zaman lafiya, ba mai tayar da fitina ba.
Nura y ace a yanzu zai iya yin takalma ya rika saidawa, a matsayin sana’ar dogaro da kan sa.
Shi ma Abana Ali, dan shekaru 62, ya yi nadamar yin mu’amala da Boko Haram. Sannan kuma ya yi rokon a yafe masa.
“Ba da son ran mu mu ka shiga Boko Haram ba. Tilasta ni aka yi. Kuma saboda na manayan ta, ba su zuwa yaki da ni.
“Akasari a gida ake barin mu, mu nayi musu ayyukan wahala. Sannan sun maida mu bayin da ke musu aiki su na azabtar da mu.”
Ya ce haka su ka shafe tsawon lokaci su na shan azaba a hannun Boko Haram, har zuwa lokacin da sojoji suka kai musu wani hari kubutar da su.
Wani mai suna Bukar kuwa cewa ya yi, babu wata riba ga shiga Boko Haram, sai da-na-sani da kuma wahala da aikata barna.