Tsoron yin gamo da masu garkuwa da mutane ya sa an rika murza gashin baki, ana ciccin magani wajen siyan Tikitin jirgin kasa a Rigasa

0

Domin gujewa fadawa hannun masu garkuwa da mutane a titin Kaduna zuwa Abuja ya sa dubban matafiya yin tururuwa zuwa tashar jirgin kasa dake Rigasa domin samun tikiti zuwa babban birnin tarayya, Abuja.

Mutane dai yanzu sun gwammace su tafi Abuja a tsaye ko ta halin kaka maimakon ace wai sun rasa jirgin.

Duk da haka tikitin shiga jirgin ma ya zama sai kana da kafa ko kuma zaka iya biyan cin hanci na makudan kudi kafin ka samu wannan tikiti.

Wasu da dama sun maida hada-hadar siye da siyarwar tikitin wata babbar sana’a ce ta bude musu. Tunda akwai wadanda ko nawa ne zasu siya tikitin sai aka gano wasu daga cikin ma’aikatan hukumar na cusa kan su dumu-dumu domin ganin sun samu karin kudi wajen siyar da tikiti din.

Sai dai kuma wani abin ban takaici shine duk da irin wannan gwagwarmaya da ake yi sai ka ga manyan ‘yan siyasa, da jami’an gwamnati da masu kudi sun zo tashar cikin kwanciyar hankali sun wuce talakawa na ta kowa suna murza gashin baki a tsakanin su duk sun yi gumi wajen neman tikitin jirgin sun sulale sun shige abin su salin-alin. Daga nan jirgi ya busa hon ya kara gaba abin shi.

A ranar Talata abin bai sake zani ba domin kuwa mafi yawan mutanen da suka bayyana a tashar jirgin domin tafiya Abuja basu samu tikitin ba. Kiri-kiri jirgi ya zo a gaban su sannan ya dibi wadanda suke da gatan samun tikiti ya yi tafiyar sa.

Hakan bai yi wa mutane da dama dadi domin kuwa wasu tun da asuban farko suke tashan don su sami tafiya garin Abujan.

Wani matafiyi mai suna Sanusi Alkasim, ya bayyawa wakilin PREMIUM TIMES cewa bazai iya jiran jirgin 2 na rana ba, cewa zai koma ne ya bi motan haya a tashan Kawo. Allah ya kiyaye masa hanya kawai.

Wani ma’aikacin tashar jiragen kasa dake Rigasa da baya so a fadi sunnan sa ya ce dole a sami ambaliyar mutane a tashar saboda garkuwa da mutane da ake yi a titin Kaduna zuwa Abuja. “Yanzu kowa jirgin ya ke bi ba a bin mota kwata-kwata.

Wasu da dama daga cikin matafiyan sun koka kan yadda ake siyar da tikitin a tashar dole. Sun bada shawarar a bude kafa ta yanar gizo domin a iya siyan tikitin kai tsaye ba sai mutum ya zo tashar ba sannan kuma a siyar masa da tsada.

“Daga Abujan ma ba a samun sauki, domin haka zaka ga ana ta fama da masu siyar da tikiti na bayan fage, sannan kuma dai manyan mutane ne ke samun tikitin talaka kuma sai wada Allah yayi.” Inji Alkasim.

Share.

game da Author