Wasu sabbin takardun bayanan sa hannun kwangilar naira bilyan 2.5 ta kamfanin Pinnacle Communications Limited da Hukumar Kula Da Gidajen Radiyo Da Talbijin (NBC), sun kara tabbatar da yadda Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ke da masaniyar kwangilar tun daga farko har karshe.
Kwangilar dai NBC ta bayar da ita ne domin inganta karfin kama tashoshin gidan talbijin na NTA, ta yadda zai inganta daga na game gari wato ‘analogue’, zuwa na zamani, wato ‘digital’.
Takardun da suka fado hannun PREMIUM TIMES sun tabbatar da kudaden da NBC ta biya kamfanin Pinnacle Communications Ltd, a cikin Mayu, 2017, akwai harkalla a ciki, kamar yadda Hukumar Ladafta Ma’aikatan Gwamnati, wato ICPC ta jaddada.
A kan haka ne ICPC ta gudanar da bincike, sannan kuma ta maka Shugaban NBC, Ishaq Modibbo Kawu a kotu.
An gurfanar da shi kotu tare da shugabannin kamfanin Pinnacle Communications Ltd., da suka hada da Lucky Omoluwa da Dipo Onifade.
Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya amince tare da sa hannu a biya kudaden.
Sannan kuma an gano cewa ministan na da hannu wajen tattauna yadda za a gudanar da kwangilar da kuma wasu tafiye-tafiye da yay i kasar waje bayan an biya kudaden.
Duk da cewa jamai’an ICPC na da masaniyar akwai hannun Lai a cikin kwangilar, ba su gurfanar da shi a kotun ba.
ICPC ta bayyana wa kotu cewa yaudarar Lai Mohammed aka yi har ya sa wa kwangilar hannu, ba tare da sanin abin da ta kunsa a hakika ba.
A lokacin da jami’an bincike na ICPC suka tambaye shi, Minista Lai ce musu ya yi shi dai kawai ya sa hannu ne a kan takardun neman amincewar sa kan kwangilar, wadanda Kawu, shugaban NBC ya kawo masa domin ya sa hannu.
Sannan kuma bai musanta cewa akwai alamomi ko yiwuwar harkalla a biyan naira bilyan 2.5 da Kawu ya yi ga Pinnalce Communications Ltd ba.
Kawu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Lai Mohammed ya sa hannun amincewa da biyan kudin kwangilar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta hado wa masu karatu da tulin takardun shaidar yadda aka rika karakainar tura wa Minista Lai takardu ya na sa hannu.
A cikin takardar kwangilar, kamfanin Pinnacle ya bayyana cewa makudan kudaden da ya ce a biya, ba su yi yawa ba, idan aka yi la’akari da gagarimin aika sakon ‘signals’ ga tashoshin talbijin da za su rika yi wa masu talbijin a kasar nan.
Tun da farko kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa sai da wani jami’in ICPC ya yi tsokaci a kan kwangilar, ya ce akwai lauje a cikin nadin rawani, amma aka ki maida hankali a kan korafin da ya yi.
Wannan korafi da ya yi na daga cikin shaidun da aka gabatar wa kotu.
Zuwa yanzu dai an gabatar da shaidu 11 a gaban mai shari’a duk a kan tuhuma 12 da ake wa Modibbo Kawu da Omoluwa da Onifade, da kuma kamfanin Pinacle.
Discussion about this post