Tsarabar Madinah: Kuji Tsoron Allah A Kan Sarakunan Mu Na Musulunci! Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu Alaikum

Ya ku bayin Allah! Ku sani, Mai Martaba Sarkin Musulmi Uban Kowa Ne… Shugaban Kowa Ne, Jagoran dukkanin Musulmi ne… Kuma Shine Shugaban Majalisar koli ta Addinin Musulunci a Nijeriya. Don haka ya cancanci girmamawa, da biyayya da kuma ladabi daga dukkan kowane mutum a kowane sashe, daga wannan Daula ta Usmaniyyah, har Kasar ma gaba dayan ta, da kuma dukkanin yankin Africa, kai da ma duniya baki daya.

Babu dalilin da za yasa wasu tsagerun ‘yan siyasa, marasa tarbiyya, marasa ilimi su rinka shiga kafafen sada zumunta na zamani da gidajen rediyo da Talabijin, suna sukar Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Wallahi yin haka ba karamin jahilci bane da kuma rashin sanin girman magabata.

Kwanaki kadan da suka shude, wani jagoran Jam’iyyar siyasa na jihar Sokoto, ya jagoranci ‘yan ta’adda da ‘yan dabar siyasar sa, suna ta zagin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad, har wai don rashin tarbiyyah da rashin kunya suna ta kiran wai Sabon Gwamna Sabon Sarki.

Sai ga shi yau an wayi gari Allah ya kunyata shi, domin Allah bai ba wanda suke so nasara ba, balle suyi cin mutunci, sai yaba mai girmama shugabanni, mai girmama sarakuna iyayen al’ummah, mai tausayi da biyayya ga talakawan sa, wato Matawallen Sokoto, wanda yasan girman gidan Mujaddadi Shehu Usmanu Dan Fodiyo da kuma masarautar shi.

Sai gashi kuma yanzu wani sabon salo da ‘ya’yan waccan Jam’iyya suka shigo da shi, mutanen da suke nufin cin mutuncin Mai Alfarma Sarkin Musulmi a sokoto, shine, su biya wasu jahilai, wawaye, suna bin gari wa gari, suna bin sashen kafafen sadarwa da sauransu don aci zarafin Mai Alfarma da Martaba Sarkin Musulmi. Wannan tabbas ba karamin kuskure bane, wanda ko a wajen Ubangiji, zai iya yin hukunci a kan wadannan marasa tarbiyya da ilimi na Addini.

Wadannan mutane, masu kokarin raina muna shugabanni da sunan siyasa, ya kamata su sani, wallahi, dukkanin sarakunan mu, tun daga Sarkin Musulmi, zuwa Shehun Borno, zuwa Sarkin Gwandu, zuwa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, kai da duk ko wane sarki da kuka sani, shugabanni ne na addinin Musulunci, jagororin mu ne na addini.

Don haka, wallahi, taba su, muna daukar shi taba addini ne. Cin mutuncin su, muna daukar shi cin mutuncin addini ne. Don haka, wallahi, wawayen ‘yan siyasa, jahilai, da magoya bayansu su kiyaye wannan. Kuma su iya sani cewa, ba zamu taba zuba ido, muyi shiru ana cin mutuncin jagororin addinin mu mu kyale su ba. Domin zubar da mutuncin wadannan bayin Allah, wallahi zubar da mutuncin addinin Musulunci ne!

Don haka ya zama wajibi mu kiyaye!

Allah Yaja Zamanin Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, Allah Ya kara Kare Mutuncin shi da kujerar shi, Allah ya isar mai ga duk wani mai neman cin zarafin shi, amin.

Haka dukkanin sarakunan mu, mataimakan sa, masu martaba, ina rokon Allah ya ja zamanin su, ya taimake su, yayi masu jagora da kariya, ya kare mutuncin su da kujerun su daga wawanci da shirmen mahassada da jahilai, amin.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Birnin Madinah, Saudi Arabia. Za’a iya samun sa a: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author