TRADER MONI: Za a ci gaba ba, ko an ci zabe an wuce wurin?

0

Tsarin nan na bayar da lamuni ba tare da gindaya sharudda ba ga masu kananan sana’o’i, wato TRADER MONI, wanda gwamnatin tarayya ta shigo da shi, ya samu gagarimar karbuwa a kasar nan.

Sai dai kuma duk da haka, ya samu kakkausar suka, musamman ganin cewa ba ko’ina ake karadewa ana raba kudin ba.

TRADER MONI tsari ne da gwamnati ke bayar da lamuni na naira 10,000 ga masu kananan sana’o’i ’yan tireda, domin a kara tattafa musu samun sana’ar dogaro da kai.

Sai dai me, ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari ta fi maida hankali kan tsari a daidai gabatowar zaben shugaban kasa na 2019, ya sa an rika sukar shirin.

Da dama sun karkata a kan cewa Buhari ya maida TRADER MONI wani salon kamfen, ganin yadda kacokan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya maida hankali wurjanjan wajen rabon kudin Trader Moni a cikin kasuwannin garuruwa da dama a kasar nan.

An rika zargin gwamnatin APC cewa ta na yin kamfen ne da shirin Trader Moni, mai makon da kudin jam’iyya.

An karfafa wannan zargi ganin yadda jami’an tsaro suka sa-ido sosai a bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade, domin ganin ba a yi kamfen da makudan kudade ba a zaben 2019.

Wannan ya kashe wa jam’iyyar adawa, PDP guiwa, gabin yadda ta yi kamfen ba da cikakken karsashin da aka san PDP ta saba yin kamfen a zabukan baya ba.

A nata bangeren kuwa, APC ta rika gudanar da shirin Trader Moni bagatantan a jihohin da Buhari zai kai ziyara, kwanaki kadan kafin zuwan sa.

Mataimakin sa Osinbajo ne ya rika bi gari-gari cikin kasuwanni ya na tallata Trade Moni a lokacin kamfen.

Sai dai kuma bayan an kammala zabe APC ta sake yin nasara, an ji dif kamar an daukar ruwan sama. Babu zancen shirin kuma babu sanarwar za a ci gaba da shi.

Wannan ya sa jama’a da dama na ta tambayar junan su, shin za a ci gaba da tsarin Trader Moni ne, ko kuwa ya tabbatar shirin kamfen ne na zaben 2019, an ci zabe, shirin ya mutu, an wuce wurin?

Ina labarin wadanda aka bai wa kudaden? Dama wani da PREMIUM TIMES Hausa ta yi hira da shi kafin zabe a cikin kasuwar Wuse, Abuja, ya ce yadda tsarin ya ke, “idan ka biya shikenan, idan kuma ba ka biya ba, to ka ci ‘rabon ka’, an wuce wurin.”

Share.

game da Author