A yau ne bangaren dan takarar Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya maida kakkausar suka ga bangaren masu goyon bayan Hon. Umaru Bago.
Jiya Laraba dai ne magoya bayan Umaru Bago su ka ce ba za su janye ba su kyale Gbajabiamila shugabancin majalisa ba, sai dai a yi zabe.
Gbajabiamila ne shugabannin APC suka amince zai zama Kakakin Majalisar Tarayya, ba tare da zabe ba. Amma da yawa wasu sun ki amincewa da wannan zabi da APC ta yi a gaban Buhari.
Jiya kakakin yada labarai na kamfen din Umaru Bago, Victor Ogene, ya ce “ba za mu janye wa Gbajabiamila ba. Babu gudu, babu ja da baya, kuma babu saranda.” Haka ya bayyana.
Magoya bayan Bago sun tafi a kan cewa yankin Middle Belt ko kuma Arewa ta Tsakiya ce ya kamata ta fidar da Kakakin Majalisa, ba yankin Kudu Maso Yamma ba inda Gbajabiamila ya fito.
Gbajabiamila da dai shi ke wakiltar mazabar Surulere 1 daga Jihar Lagos. Kuma wannan zango da za a shiga, shi ne zangon sa na biyar a jere a Majalisar Tarayya.
A 2015 ma shi APC ta fitar kuma ta fitar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa.
Sai dai kuma ‘yan majalisa sun yi wa APC tutsu, inda suka zabi Bukola Saraki da Yakubu Dogara.
Mai magana a madadin Femi Gbajabiamila, mai suna Hon. Yemi Adamodu, yacew ba abin burgewa ba ne su tsaya su na sa-in-sa da abokan su ‘yan majalisa a kan neman shugabanci.
Sai dai kuma ya ce ba za su yi shiru ba, ganin yadda magoya bayan Bago suka rika maida abin kamar wani bangaranci, har da hakikicewa sun a cewa, “babu saranda babu gudu kuma babu ja da baya.”
Ya ce irin wadannan kalamai masu zafi bai kamata su na fitowa daga cikin ‘yan jam’iyyar APC ba, jim kadan bayan nasarar da jam’iyyar ta samu sakamakon hada hannu wuri daya da kowane bangare na karar nan ya yi da juna har aka samu nasara.
Martanin wanda bangaren Gbaja suka mayar cikin tsatsatsauran Turanci, sun nuna cewa babu shakka Umaru Bago mutum ne mai mutunci kuma nagari.
Amma fa martanin da aka yi wa Gbajabiamila a jiya Laraba, akwai alamar cewa wani ne ya bugi kirji kawai ba da sanin sa ba Ogene ya rubuta kalaman, wanda suka nuna cewa wai ba da sanin Shugaba Muhammadu Buhari shugabannin APC suka ce a zabi Sanata Ahmed Lawan da Hon. Femi Gabjabiamila ba.
Amadodu ya kara da cewa wannan furuci cin fuska ne da raini da kuma cin zarafin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce APC na gudun kada a maimaita irin ta 2015, shi ya sa ta fitar da Lawan da Gbajabiamila a matsayin shugabanni domin a zama tsintsiya madaurin ki daya.
Discussion about this post