Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya maida wa jagoran jam’iyyar APC ,Bola Tinubu martani, bayan da ya zarge shi da Bukola Sarki da laifin kawo tsako ga kasafin kudi har tsawon shekara hud, da kuma cusa murda-murda a cikin kasafin domin azurta kan su.
Yakubu Dogara ya ce Tinubu na da wani hali na matsanancin son girma da son mulki da kuma ajendar yi wa komai kaka-gida.
A yau Talata ce ya maida wannan martanin ta hannun kakakin yada alabarai na sa, Hassan Turaki.
Tinubu ya zargi Saraki da Dogara cewa:
“Mun dai san irin muhimmancin da mukamin Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya ke da shi wajen ganin Shugaban Kasa ya cimma kudirorin da ya ke son cimma. Ya kamata mutum ya kalli shekaru hudun da aka shafe sannan ya dubi darasin da aka koya daga abubuwan da suka rika faruwa, inda shugabannin Majalisar Dattawa suka rika zame wa shugaban kasa da gwamnati karfen-kafa, alakakai tare da yi wa harkokin tafiyar da gwamnati kafar-ungulu.
“Ku dubi dai yadda Saraki da Dogara da ’yan amshin-Shatan su suka rike wa kasafin kudi makogaro tsawon shekaru hudu. Sun rika kin sakin kasafin kudi, kuma suka rika cusa ayyukan su wadanda za su rika kudancewa a rana daya daga cikin kudaden gudanar da ayyukan.
“Abin na su ya yi munin da har kudaden da za a yi wa al’umma ayyukan ci gaba suka rika zabtarewa. Saboda haka bayan mun shafe shekara takwas su na hana ruwa gudu, ya kamata mu yi duk irin abin da za mu iya domin kauce wa maimaita fadawa hannun Shugabannin Majalisar da suka rika hana ruwa gudu tsawon shekaru hudu.
Yayin da Saraki ya maida na sa martanin tun jiya, Dogara kuma a yau Talata ya kalubalanci Tinubu da ya kawo hujjojin zargin da ya yi musu.
A kan zargin cushen ayyuka a cikin kasafin kudi, Dogara ya ce wannan rashin sani ne da za rika zargin Majalisar Tarayya.
Ya ce: “Ai dama kasafin kudi doka ce, kuma aiki ne na majalisar tarayya. Ita ke da alhakin tsara shi yadda ya dace, ba bangaren gwamnati ba.”
Dogara ya ce akasari ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ministocin ne ke janyo tsaiko ga kasafin kudi. Ta yadda za su tsara gidogar da ba su iya zuwa su kare abin da suka yi a cikin kasafin.
Sannan kuma ya kara da cewa sau da yawa za a kira su ba gabann kwamiti su kare kasafin kudi, amma sai su yi ta kame-kame ko kuma a yi ta kulli-kurciya da su.
Sannan kuma ya ce Tinubu na da wata ajanda ta sa ta son kankane Najeriya. Ya caccake shi da cewa ya sani ita fa Majalisar Tarayya ba ‘yan amshin-Shata ba ne, kuma ba gungu ne na sankira da ‘yan ma’abban Tinubu ba.
Don haka ya ce ba zai yiwu su zura ido mutane irin su Tinubu sun jefa majalisa dungurugum a cikin aljihun su ba.
Daga nan Dogara ya fayyace dalla-dalla irin ayyuka da kudirorin da majalisa ta gabatar wadanda a tarihinn siyasa daga 1999 zuwa 2015 ba a yi zangon majalisar da ta yi rawar gani kamar ta 2015 zuwa 2019, wadda shi Dogara ke shugabanta.
Discussion about this post