TASHIN HANKALI: Wai shin Kajuru ta gagari gwamnati da jami’an tsaro ne? Daga Aisha Yusufu

0

Tashin-tashinan da ya addabi mutanen jihar Kaduna musamman mazauna yankin Kajuru ya na neman ya fi karfin gwamnatin jihar Kaduna da jami’an tsaron kasar nan.

Ba tun yanzu ba ake ta fama da matsalar barkewar rikice-rikice a wannan karamar hukuma sai dai a kullum za aji an kai dauki ko kuma an fatattaki wadanda suka tada rikici ko husuma ba tare da an bayyana wadanda aka kama a gaban hukuma ba sannan a hukunta su kamar yadda doka ta gindaya.

Fitacciyar kasuwar magani da ta yi suna wajen kasuwanci da cinikayya sannan kuma mahada ce na manyan manoma da ‘yan kasuwa yanzu ta zama shiga da alwalanka domin ako wani lokaci mahara za su iya far wa mutane suna cin kasuwa su kashe na kashewa su yi tafiyar su.

Gwamnati da jami’an tsaro su kan yi gaggawar yin shelar kama wadanda ke da hannu wajen aikata wannan ta’asa sai dai daga wannan lokaci ba za aka sake jin komai ba a kai.

Kusan kullum sai kaji an kashe wani ko kuma an babbake wasu kauyuka. Baban dalilin da ya sa ake samun irin haka kuwa shine ko don akai ramuwar gayya.

Idan wancan kabilar ta far wa makwabciyar ta ko bayan an sasanta su ne kwanaki kadan sai kaji wadancan suma sun far wa ‘yan uwan su.

Gwamnati da jami’an tsaro na nuna kamar abin ya gagara ne. An taba saka dokar hana walwala wanda a cikin wannan hali ne ma aka far wa wasu kauyuka. Idan ba a iya samar wa mutane tsaro ba a lokacin da suke bukata yaushe za a iya samar musu?

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya takarawar gani wajen ganin an kawo karshen wannan tashin hankali sai dai har yanzu babu wani nasara da za a iya nunawa wai an samu duk da kokarin da yake yi na kawo karshen haka. Idan ance an fatattaki masu tada wannan zaune tsayi ya sai kaji kuma ya sake barkewa a wani gefen.

Yanzu dai wannan karamar hukuma ta yi kaurin suna a kasar nan. Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne aka kashe wata yar kasar Birtaniya a gidan shakatawa na Kajuru sannan a ka yi garkuwa da mutane da dama a wannan gida.

Dama dai karamar hukumar Birnin Gwari na fama da irin wannan tashin hankali musamman na mahara da masu garkuwa da mutane. Abin dai ya baci matuka da yanzu dole mutane su koma ga Allah domin ga dukkan alamu abin ya fi karfin gwamnati da jami’an tsaro.

Share.

game da Author