TAMBAYA: Wani addu’a ne yafi dacewa matafiyi ya yi? Tare da Imam Bello Mai-Iya
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
A musulunce tafiya nau’i uku ce: tafiyar da ake yabo: kamar tafiya don sauke farali, neman ilimi sada zumunta…., tafiyar da ake zargi da ki, kamar tafiyar safarar muggan kwayoyi. Na karshe shi ne tafiyar da ta hallata kamar tafiya domin kasuwanci ko yawon bude ido. Nau’in tafiya na farko da na karshe bawa nason lada in ya tsarkake niyyarsa.
Mustahabi ne kafin tafiya a yi Sallar Istikhara, jaddada tuba, kyautata niyya, sauke nauyi da biyan hakkoka, zaben nagartattun abokanen tafiya, da ayyana lokacin tafiya.
A dawowa kuwa Mustahabbi ne, Gaggauta dawowa gida bayan kamala bukatatar tafiya, da sallatar raka’a biyu a masallaci kafin shiga gida kuma kar a afkawa iyalai cikin dare batare da sani ba.
ADDU’AR TAFIYA
Imam Muslim ya ruwaito daga Ibn Umar: Matafiye zai yi wannan addu’a a lokacin da yahau abin hawansa da nufin tafiya:
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Subhanal ladhi sakkhara lana hadha wama kunna lahu muqrinina, wa inna ila rabbina la munqalibuna,. Allahumma inna nas-aluka fi safarina hadhal birri wat taqwa wa minal ‘amali ma tardha. Allahumma hawwin ‘alaina safarana hadha watwi ‘anna bu’dahu . Allahumma antas shahibu fis-safari wal khalifatu fil-ahli.
Allahumma inni a’udhubika min wa’tha’is safari wa ka’abatil manzari wa su-il munqalabi fil mali wal ahli. Idan zai dawo daga tafiyar ta sa, sai kuma ya fadi wannan addu’ar, ya kuma kara da cewa: Ayibuna, ta’ibuna, ‘abiduna li-rabbina hamiduna.
الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر. سُبْحانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَذَا
وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَ وَإِنَّا إِلَى رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ .
اَللَّهُمَّ اِنَّانَسْأَلُكَ فِى سَفَرِنَا هَذَا البِرَّ وَ لتَّقْوَى
وَمِنَ الْعَمَلِ مَا تَرْضَى , اَللَّهُمَّ هُوِّنْ عَلَيْنَا سَفَرَنَا
هَذَا وَاَطُوْ عَنّا بُعْدَهُ . اَللّهُمَّ اَنْتَ الصَاحِبُ فِى
السّفَرِ وَالْخَلِفَةً فى الأَهْلِ. اللَّهُمَّ اِنِّى اَعُوْذُ بِكَ
مِنْ وَعْثَاءِ السَّفَرِ وكَابَةِ الْمَنْظَرِ وَسُوْءِ الْمُنْقَلَبِ
فِى الْمَالِ والأَهْلِ. وعند الرجوع يتكرر الدعاء ونضيف عليه “آيبون،
تائبون، عابدون، لربنا حامدون” رواه مسلم
Fasarar Addu’ar tafiya Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Allah shi ne mai girma, Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan abin hawa, kuma ba mu kasance masu iya rinjaya gareshi ba. Kuma lalle mu ga Ubangijin mu hakika masu komawa ne. Ya Allah! lalle muna rokon kyawawan al’amura da tsoronka a wannan tafiya ta mu, kuma muna rokon aiki wanda aka yarda da shi. Ya Allah! ka sawwake mana wannan tafiya ta mu, ka nade mana nisanta. Ya Allah! kai ne ma’abocin mu a cikin wannan tafiya, kuma kai ne halifan mu a cikin iyalan mu. Ya Allah! Ina neman tsarinka daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya bacin rai, da kuma mumnunar makoma ga iyali da dukiya. Idan zai dawo daga tafiyar ta sa, sai kuma ya fadi wannan addu’ar, ya kuma kara da cewa: Mu masu komawa ne, masu tuba masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijin mu.
ADDU’AR MATAFIYI GA MAZAUNI
Ina sanya ku a cikin kiyayewar Allah, wanda abin da aka sa a cikin kiyayewarsa ba ya tozarta أستودعكم الله الذي لا تضيع ودائعه
ADDU’AR MAZAUNI GA MATAFIYI
Ina bai wa Allah ajiyar addinin ka da a manarka da kuma ayyukan da ka ke cikawa a kan su. Allah ya yi maka guziri da takawa, ya gafarta maka zunubanka, ya saukake alhari a gare ka a duk in da kake.
أستودع الله دينك وأمانتك وخواتيم عملك , زودك الله التقوى ، وغفر ذنبك
ويسر لك الخير حيث ما كنت