TAMBAYA: Wane abubuwa ne ya fi zama muhimmi miji ya rika hana matar sa yin su? Tara da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Wane abubuwa ne ya fi zama muhimmi miji ya rika hana matar sa yin su?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Zamantakewar aure alaka ce mai matukar daraja da kima, shari’ah ta taskaceta da dokoki na adalci. An gina aure ne akan taimakon juna
acikin rayuwa, adini da duniya. Allah yace: ku taimaki juna acikin abin alhairi da imani. Musulunci ya fayyace hakin ma’aurata, idan an
karanci addini kuma anfahimce shi abi sani kuma akayi aiki da shi, to za’a zauna lafiya cikin nishadi da walwala. Amma idan ma’aurata suka
walakanta hokkokin aure, to al’uma gaba daya za ta tarwatse, ta dai-daice, ta lalace, fasadi ya watsu, muyagon laifuka su yadu
sakamakon tauye hakkin daya daga cikin ma’aurata.

Hakika miji yanada hakin hana iyalinsa duk wani abinda shari’ah ta hana. Kamar yadda kuma zai iya hana duk abinda zai tauye masa hakkinsa a gurinta. Kuma yanada ‘yancin hana duk abinda zai cutar da gidansa ko iyalinsa ko dukiyarsa. Sannan miji nada karfin hana duk abinda baici
karo da shari’ah ba. Allah ya ce: duk hakkin da maza su ke dashi akan matansu, suma matan su nada kwatankwacinsa akan maza kamar yadda
shari’ah ta tanada. Amma maza sunada fifiko (Bakara 228). Kur’ani ya ce: maza sune masu tsayowa akan lamarin mata (Nisa’i 34).

Malamai su kace wadannan ayoyin suna nuna cewa maza ne shugabbanin iyalansu, kuma mata su zaamo masu yin da’a agaresu. Wajibi ne mata ta
yi biyyaya ga mijinta matukar babu sabon Allah acikin haninsa ko umurninsa. Amma hakan kuma wajibine ya ka sance akan ginshikin nan na
“ba cuta ba cutarwa” idan kawai cuta ko cutarwa, to hanin miji ba lalle bane yayi tasiri.

A takaice, dole ne miji yana matarsa duk monanan abinda shari’ah da hana. Kuma miji nada damar hana wasu ibadun da ba wajibi bane, zai iya
hana duk wani abinda bayasu matukar babu tauye hakki aciki. A gefenta ita mata dole ne ta yi biyyaya ga miji matukar babu sabon Allah kuma
cuta ba cutarwa.

Su kuma maza su ji tsoron Allah, su tsare duk hakkokin iyalansu tare da ihsani ga matansu, bisa ka’idar nan ta “ba cuta ba cutarwa”. A
hudubar Annabi SAW ta karshe, ya umurci maza da su kyautata zamantakewar aure, kamar yadda Al-Kur’ani yace ku kyautata, lalle
Allah yana son masu kyautatawa.

Ya Allah! Ka albarkaci gidajenmu da kyakkawan zamantakewa. Amin.

Share.

game da Author