Tallata Bidiyon Zargin Madigo Da Hadiza Gabon Tayi Abun Kunya Ne Ga Daular Usmaniyya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Tirrrrrr! Irin abubuwan da suke faruwa a tsakanin Hadiza Gabon da Amina Amal ya zama abun kunya a cikin Hausawa da duniyar musulunci.

Amma ban yi mamaki ba saboda dama mutane suna yiwa da yawa daga cikinsu kallon abun da yafi haka ma duba da yadda rayuwar su.

Gaskiya wasu suna gani kamar galibin matan fim sun fi kamun kai a fim fiye da rayuwarsu ta waje.

Tun lokacin da aka samu bidiyon batsa da wata yar fim tayi a shekarun baya sai mutane suka qara yadda da abun da suke zargi.

Abun tambaya a nan shine, wai shin basu da iyaye ne a raye? Anya suna daukar izina akan wadanda suka yi tashe kafin su?

Duk tashen da kika yi a fim ko rashin mutunci watarana zaki zama ‘Soriye’ tunda kece ‘yar autar mata ba.

Mu hausawa ne ‘yan arewa, wawalidin wamawalada, gaba da baya, kuna kunyata mu a idon duniya.

Abun kunya yau an wayi gari Hadiza Gabon tana tuhumar Amina Amal akan madigo, har da haskawa a bidiyo saboda tsabagen rashin kunya, to shi kansa daukar abun da suka yi rashin mutunci ne domin zai rage kwarjinin kalmar “Madigo” ne a wajen ragowar yara na gida da aka killacesu ake basu tarbiya.

Gaskiya zamu fara yi musu Allah ya isa kwanannan akan irin wannan rashin mutuncin. Wai shin babu dokoki ne a Kannywood din? Ko kuma matan sun fi karfin mazan fim din saboda suna samo kudi a wajen manya?

Amma abun mamaki sai naji wasu suna zagin Kanawa, wai su Gabon yan Kano ne, wannan kuskure ne saboda dukkansu babu ‘yar Kano saidai ‘yan ci-rani, daga Amina Amal har Hadiza Gabon shigo mana suka yi, wata daga Gabon wata daga Kamaru.

Ai a cikin mata ‘yan fim din hausa da wuya ka samu cikakkiyar bakanuwa guda 5, ko kin fara fim sai mun lallabaki mun yi miki aure insha Allah.

Gaskiya akwai matsala fa, ba mu ce kada su yi sana’ar su ba, babu abun da ya shafe mu da sana’ar su, amma gaskiya idan ba ayi wa abun tubka ba bamu san me zasu yi ba a gaba.

Malamai da Sarakunan daular Usmaniyya (Arewacin Najeriya) dole su shiga cikin lamarin don ya shafi addini da al’ada.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author