SUNAYE: Maharan da aka kama bisa zargin kashe sarkin Adara, Maiwada Galadima

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama wasu da ake zargin sune suka kashe sarkin Adara, Maiwada Galadima.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Frank Mba ne ya sanar da haka inda ya kara da cewa an kama Abubakar ibrahim a garin rigachikum dake karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

An kama Ibrahim ne ta dalilin kama wani shugaban masu yin garkuwa da mutane mai suna Salisu Abubakar da aka yi inda ya rika tona musu asiri.

Sauran wadanda aka kama sun hada da Johnson Okafor, 44; Shaibu Iliyasu, 20; Ishaik Dabo,38; Mohammed Nasiru, 25; Aminu Haruna, 25; Shafiu Gudau, 25; Auwalu Hamisu, 24; Ado Ya’u, 35; Ibrahim Yusuf, 30; Ibrahim Audu, 22; Salisu Ajah, 50; Magaji Abubakar, 27; Salisu Ali, 18, da sauran su.

Frank ya kara da cewa an kwato bidigogi kirar AK 47 da guda 22 da harsasai masu dama.

Sannan kuma jami’an ‘yan sanda na nan na ci gaba da farautar irin wadannan bata gari domin kawo karshen ayyukan ta’addan ci a jihohin dake fama da haka.

Share.

game da Author