SUNAYE: El-Rufai ya bayyana sabbin nade-nade

0

Gwamnan jihar Kaduna ya sanar da sabbin nade-nade da yayi a jihar ranar Litini.

Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a takarda da ya saka wa hannu ranar Litinin.

A sabbin nade-Naden, gwamna El-Rufai ya nada Muhammad saidu, a matsayin sabon kwamishinan Kudi na jihar. Saidu ya sauka daga kujeran shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ne zuwa ma’aiakatar kudin jihar.

Sauran wadanda aka nada sun hada da Idris Nyam Akanta Janar din jihar, Umar Waziri kuma shine sabon shugaban hukumar saka jari na jihar Kaduna sannan shi kuma Salisu Suleiman zai rke kujerar shugaban ma’aikatan fadar gwamnati har zuwa a nada wani.

Hafiz Bayero shugaban Hukumar kula da Kasuwannin jihar da kuma Hadiza Usman Muazu a matsayin mai ba gwamna shawara kan Harkokin gwamnati.

Share.

game da Author