Kungiyar Masu Casar Shinkafa ta Najeriya (RIPAN), ta koka cewa a cikin watanni uku kacal da suka gabata, an yi fasakwaurin shinkafa zuwa cikinnkasar nan za ta kai sama da buhunna miliyan 20.
Shugaban RIPAN Mohammed Maifata ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke wa manema labarai bayani a Abuja, dangane ya yawaitar shigo da shinkafa a cikin kasar nan, duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta haramta shigo da ita.
Ya kara da nuna takaicin cewa yayin da milyoyin ‘yan Najeriya suka zuba jari a cikin kasar nan wajen inganta noma da cashe shinkafa, abin bakin ciki shi ne yadda a cikin watanni uku kadai aka shigo da sama da metric tan na shinkafa har milyan daya.
Ya ce ya na daidai da buhu milyan 20 kenan mai cin Kg 50.
Ya kara da cewa masu sumogal na karya kanana da manyan manoman shinkafa, kuma su na janyo wa Najeriya asarar bilyoyin kudade zuwa kasashen waje, tare kuma da asarar kudaden shiga cikin kasa.
“ya ce abin mamaki ne duk da irin matakan tsaron da ake sa wa, amma kan iyakokin Najeriya sun koma dandalin safarar shinkafa sannan kasuwannin cikin kasa cike suke makil da shinkafar da ake sumogal daga kasashen waje.
Ya ce wannan matsala za ta gurgunta shirin noman shinkafa a kasar nan, sannan kuma ta kassara kanana da manayan manoman shinkafa da masu kasuwancin ta a cikin kasa.