Sojojin Operation Harbin Kunama sun samu galabar kashe ‘yan bindiga hudu a cikin Karamar Hukumar Shinkafi.
Babban Kwamandan su kuma Shugaban Bataliyar Sojojin Runduna ta 8 da ke Sokoto, Hakeem Otiki ne ya bayyana haka.
Ya yi wannan sanarwa ce a lokacin da ya ke hira da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Sai dai ya ce an jima wa sojoji shida rauni, amma ana ci gaba da kula da su.
Ya kara tabbatar da cewa sojojin sama tare da taimakon sojojin kasa da wasu zaratan sojojin Jamhuriyar Nijar, sun samu galabar fatattakar mahara da dama a jihohin Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara, har ma da wasu sassa a cikin Jamhuriyar Nijar.
Ya ce an kashe mahara kuma an ji wa wasu masu yawa raunuka ta harbin bindiga, tare da damke wasu a Kamarawa, kusa da Shinkafi.
Sannan kuma ya ce sojojin ‘Operation Harbin Kunama sun samu nasarar kama wasu mutane bakwai da ake zargi su na yi wa mahara da barayin shanu da gwarkuwa da mutane leken asiri.
Kwamandan ya ce zaratan sa za su ci gaba da yin hobbasa har sai sun kakkabe maharan da su ka addabi yankunan jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara da Kebbi.