Mahukuntan Sojan Najeriya sun bayyana cewa a ci gaba da hare-haren “hana Boko Haram samun damar yin barci”, sun bindige 27 a wani farmaki na hadin guiwa da aka kai tare da sojojin kasar Kamaru.
An kai masu farmakin ne a ranar Asabar, kuma an samu manyan makamai da harsasai da kayan sojoji a hannun su, kamar yadda sanarwar da kakakin sojoji ya bayar a yau Litinin.
Ya ce an gwabza yakin ne a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu da Bukar Maryam da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.
Kakakin ya ce farmakin da aka kai musu na daga kokarin kakkabe sauran burbushin ’yan ta’addar da suka rage wanda ake ganin an gana da su gaba daya.
Ana yin shirin ne a karkashin gamayyar dakarun Najeriya da na Kamaru a kan kokarin kawo karshen Boko Haram.
An kwato motocin harba manyan bindigogi biyar, baburan hawa masu yawa, bindiga biyar samfurin AK47, Libarba samfurin Galil, da GPMG, wato bindigar nan tashi-gari-barde.
An kuma samu manyan bindigogin harbor jiragen yaki guda biyu, bindigar harba roket, motoci da sauran makamai.
Kakakin sojoji Sagir Musa, ya ce ba a samu ko da sojan Najeriya ko na Kamaru daya da ya rasa ran sa ko ya ji rauni ba.