Sojoji sun ritsa maharan Zamfara, sun yi musu kisan rubdugu

0

PREMIUM TIMES ta samu rahoton wani kisan rubdugu da sojojin Najeriya suka yi wa mahara a kauyen Tsanau cikin Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce sojojin sun kewaye maharan wajen karfe 1 na rana, inda suka datse duk wata hanyar shiga da fita kafin su fara afka wa maharan.

Sun kuma ce sojojin sun je kauyen dauke da manyan makamai.

“Yayin da wasu sojojin suka tare hanyar shiga da ta ficewa daga garin, wasu kuma sun kutsa cikin kasuwar kauyen inda suka darkaki mahara wadanda ke yawon su kai tsaye a cikin kasuwar dauke da bindigogi.

“Sojoji sun kashe mahara da dama, wasu kuma sun jefar da bindigogin su, suka fade keya, ganin yadda sojoji ke ta ratattaka masu wuta.

“Ni dai ba zan ce ga iyakar wadanda aka kashe ba, amma an kashe da yawa, wasu kuma sun tsere da harbin harsasai a jikin su. Lokacin da sojojin suka zo, ba su sha wahalar shaida maharan ba, saboda dukkan su suna yawon su kai tsaye dauke da bindigogi.” Haka wani mazaunin kauyen wanda ya nemi a sakaya sunan sa ya shaida.

Ya kuma kara da cewa, “Da idon mu mun ga an kama mahara guda hudu, daya daga cikin su ma wani mai kemis ne da ke kauyen, wanda ke bai wa mahara magani ko sa musu magani idan sun ji rauni.

Kakakin Yada Labarai na Sojojin Zamfara, Clement Abiade, ya tabbatar da rahoton karkashe maharan, kuma y ace har yanzu ana ci gaba da darkakar su ana bi ana kashewa.

Ya kuma ce ba zai yi sauri ko gaggawar sakin wani bayani ba tukunna, saboda bas u gama samun bayanai daga filin daga ba.

Ranar Asabar PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa mahara sun cika kauyukan Jaja, Rukudawa da Tsanu a Karamar Hukumar Zamfara, kuma yawaon su kai tsaye a cikin mutane, dauke da bindigogi, ba tare da an tunkare su ba.

An ce maharan sun arto ne daga cikin dazukan da sojoji suka fatattake su, su kuma mazauna kauyukan suka kyale su domin tsoro.

Zamfara na fama da hare-hare da kashe na mahara ‘yan bindiga masu kashe mutane, satar shanu, garkuwa da banka wa kauyuka wuta. Kananan Hukumomi takwas daga cikin 14 da ke Zamfara, duk su na fama da ‘yan bindiga.

Shekara kusan goma kenan ana fama da tashe-tashen hankula a Zamfara, harvabin ya bulla a Birnin Gwari da wasu kananan hukumomi na Katsina.

Share.

game da Author