Dakarun Najeriya sun samu nasarar kashe ‘yan bindigar Zamfara shida, sannan kuma sun kama wasu mutane 18 da ake zargi da kai wa mahara rahoto kan wadanda za su yi garkuwa da su.
Daraktan Riko na Yada Labarai Sagir Musa, ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.
Daga cikin wadanda ke aika wa mahara da bayanai na sirri, ciki har da wani dagaci da aka ce shi ma aikin sa ke nan.
Jama’ar Zamfara da na Jihar Katsina sun dade su na kukan cewa ana hada baki da makwauta, ’yan uwa ko wasu ‘yan gari ko kauyen da suka san sirrin wanda za a yi garkuwa da shi, domin a samu kudin fansa a raba tare da su.
Sannan kuma irin su ne ke kiran mahara a waya su na sanar da su cewa su shirya jami’an tsaro na kan hanyar neman su, ko kuma su gudu.
Sagir ya ce an kashe ‘yan bindigar shida ne wani kauye mai suna Kirsa da kuma Sunke da ke cikin Karamar Hukumar Anka, Jihar Zamfara.
Akwai kuma inda aka kashe wasu kauyen Doka da Mutu cikin Karamar Hukumar Gusau.
Ya ce an kama bindigogi da babura biyar a hannun su.