Mambobin Majalisar Tarayya daga Jihohin Tsakiyar Arewa, da aka fi sani da ‘Middle Belt’, sun bijire wa shugabannnin jam’iyyar APC wadanda suka ce Femi Gbajabiamila ne za a zaba Sabon Kakakin Majalisar Tarayya.
Sun bayyana haka ne a yau Laraba a Majalisar Tarayya, kuma suka sha alwashin ci gaba da fito da Hon. John Dyegh a matsayin dan takarar su.
APC ta ce an bar wa Femi Gbajabiamila mukamin Kakakin Majalisar Tarayya, yayin da aka bar wa ‘Middle Belt’ mukamin Mataimakin Kakakin Majalisa.
‘Yan Majalisar da suka fandare din sun hada da dukkan wakilan APC da na PDP wadanda suka fito daga Middle Belt.
Dukkan su sun bayyana cewa basu gamsu da zabin da APC ta yin a Gbajabiamila ba. Gbajabiamila dai mamba ne mai wakiltar jihar Legas, kuma shi ne Shugaban Masu Rinjaye a zaman yanzu haka.
Dyegh din ne da kan sa ya fitar da sanarwa, kuma ya yi magana a gaban manema labarai a Majalisa a yau Laraba.
Ya ce ba a su zabi kowa ba said an shiyyar su, wato Arewa ta Tsakiya.
Arewa ta Tsakiya ta kunshi Jihohin Filato, Neja, Kwara, Kogi, Benuwa, Taraba.
“Mu fa ba fada mu ke yi da APC ba, sam ba fada mu ke da jam’iyyar APC ba. Ba kuma za mu yi fada da. Amma fa mun ba jam’iyya dama ta duba irin tsarin rabon shugabancin da aka yi ga shiyyoyi.”
Haka Dyeh, wanda ke wakiltar Gboko/Tarka ta Jihar Benuwai ya shaida wa manema labarai.
“Matakin da jam’iyya ta dauka na ko-ka-bi-ko-ka-bi-da-kai, sam ba dimokradiyya ba ce. Mu na da ’yancin da za mu nemi takara, ehe.”
Ya ce baya ga dimbin kudir’un da Arewa ta Tsakiya ta samar wa APC, har yau yankin bai taba samar da Kakakin Majalisar Tarayya ba, tun bayan dawowa mulkin Dimokradiyya cikin 1999 zuwa yau.
Discussion about this post