SHUGABANCIN MAJALISA: Gwamnan Barno ya gurgunta takarar Ndume, ya goyi bayan Ahmed Lawan

0

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya bayyana cewa duk da yake Sanata Ali Ndume dan uwan sa ne, dan Jihar sa, ba zai yi wa uwar jam’iyyar APC tawaye ba.

Jam’iyyar APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa, yayin da Sanata Ndume ya ce bai yarda ba, zai tsaya takara, kuma zabe za a yi ba nadi daga cikin jam’iyya ba.

Ndume dan Jihar Barno ne, shi kuma Lawan dan Jihar Yobe ne.

Shettima ya yi wannan jawabi ne yayin da Kungiyar Sanatoci Masu Goyon Bayan Lawan suka kai masa ziyara a gidan sa na Abuja, a jagorancin Sanata Ahmed Lawan.

Daga nan ya ce a matsayin sa na mai biyayya ga jam’iyyar APC, ya amince ya bi umarcin da jam’iyya ta bayar.

Daga nan sai ya ce yawancin sanatocin APC sun yi nasara ne musamman nan Arewa saboda biyayyar su ga Shugaba Muhammadu Buhari. Don haka kada su kauce daga abin da Shugaba Buhari ya zaba.

“Ni ne gwamna a Barno, kuma kafin na yanke wannan hukunci sai na tuntubi shugabanninmu daga Barno, kuma muka yanke shawarar cewa Sanata Ahmed Lawan za sugoya wa baya.

“Ya kamata mu dubi gaskiya. Muhammadu Buhari shi kadai ne dan takarar da mafi yawan mu daga Arewa muka ci albarkacin sa mu ka yi nasara. Amma ba don haka ba, iri na ma ba zai iya zuwa Majalisar Tarayya ba.

“Duk da cewa jiha daya na fito da Ndume, kuma na yarda cewa siyasa tushen ta a karkara ya ke, kuma ai siyasa ta mamaye kasa baki daya.

Shettima ya ce amincewa da Lawan da Jihar Barno ta yi ba ya na nufin sun raba hanya da Ndume ba.

Sannan kuma ya ce sun amince da Femi Gbajabiamila ya zama shugaban majalisar tarayya.

Har yanzu dai Ndume bai ce ya janye ba, kuma akwai sanatoci da dama masu goyon bayan sa. Su na cewa dole sai dai a yi zaben shugaba a majalisa, ba a yi musu dauki-dora daga cikin jam’iyya ba.

Share.

game da Author