Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya karyata maganganun da ake ta yadawa cewa ya na goyon bayan Sanata Ahmed Lawan da Hon Gbajabiamila ne don ya share wa kan sa hanyar zama dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, a zaben 2023.
Tinubu ya ce ya na goyon bayan a zabi Lawan da Gbajabiamila ne saboda mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya, yadda zai samu nasarar gudanar da mulki a zangon sa na biyu.
Ya ce an yi kuskure a 2015, inda aka yi sakaci har Sanata Saraki da Hon. Dogara suka zama shugabannin majalisa, inda suka shafe shekaru hudu su na rike kasafin kudi tare da kawo tsaiko kan muhimman ayyukan raya kasa da Shugaba Buhari ya sha alwashin samar wa ’yan Najeriya.
Tinubu ya ce kwata-kwata wannan ba gaskiya ba ne a ce wai ya na azarbabin neman takarar shugabancin kasar nan.
A cikin wata takarda da ofishin Tinubu ya fitar, wadda Jami’in Yada Labarai Tunde Rahman ya sa wa hannu, Saraki ya ce irin yadda akidar siyasar ta ta sa gaba ta zama shaida a gare shi cewa shi ba mutum ne mai kwadayin mulki ba.
Ya ce tun bayan da ya gama wa’adin sa na gwamnan jihar Lagos daga 1999 zuwa 2003, bai sake neman wani mukamin siyasa ba.
Ya ce ya maida hankali ne wajen ganin ya kafa jam’iyyar da za ta bangaje jam’iyyar PDP daga mulki. Wannan nasara ce ya ce ya samu a 2015, bayan ya hada guiwa da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ma mutum ne mai kishin ci gaban kasar nan kamar sa.
Tinubu ya ce Saraki da Dogara sun yi duk yadda suka yi suka zama shugabannin majalisa, inda tare da ‘yan koren su suka zame wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari alakakai, suka rika maida mata mata agogo baya tare da kawo tsaikon gudanar da wasu muhimman ayyuka.
“To a kan haka ne za a kalli matsayar da ta sa Asiwaju ya goya wa wasu baya domin su kasance shugabannin Majalisar Tarayya. Kuma a haka za a fassara nufin sa da fahimtar sa. Ashe kenan ba za a yi mamaki ba don ya goyi bayan matsayar da Shugaban Kasa da kuma jam’iyyar APC suka dauka. Kuma hakan da ya yi ba laifi ko aibi ba ne. A matsayin Asiwaju na dan jam’iyya mai kuma yi wa jam’iyya biyayya, zai yi babban kuskure idan ya kauce daga turbar da shugaban kasa da jam’iyya ke so a bi.
“Mun dai san irin muhimmancin da mukamin Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya ke da shi wajen ganin Shugaban Kasa ya cimma kudirorin da ya ke son cimma. Ya kamata mutum ya kalli shekaru hudun da aka shafe sannan ya dubi darasin da aka koya daga abubuwan da suka rika faruwa, inda shugabannin Majalisar Dattawa suka rika zame wa shugaban kasa da gwamnati karfen-kafa, alakakai tare da yi wa harkokin tafiyar da gwamnati kafar-ungulu.
A karshe ya ce wauta ce da rashin tunani har wasu su rika yin tunanin cewa goya wa shugabannin majalisar baya zai iya kai mutum nasara ga neman wani mukami a kasar nan, musamman mukamin shugaban kasa.
Tinubu ya ce akwai matukar bukatar goyon baya ga Buhari domin ya rika tafiyar da gwamnati ba tare da yawan rikici ko sabani da majalisa ba.
Ya ce ta hanyar da kawai za a yi nasarar haka, ita ce a tabbatar da an zabi shugabannin da suka dace da rike mukaman da suka dace su rike a Majalisar Tarayya.